Home General Ba a biyan haraji yadda ya kamata a Najeriya – Bill Gates

Ba a biyan haraji yadda ya kamata a Najeriya – Bill Gates

Hamshaƙin attajirin nan na Amurka, Bill Gates ya ce ba a karɓar haraji yadda ya kamata a Najeriya.

Yayin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki kan abinci mai gina jiki da wata ƙungiyar matasan Afirka ta shirya a Abuja, shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates, ya ce nan da wani lokaci mai zuwa, Najeriya na iya zama babbar ƙasar da ke fitar da abinci zuwa kasuwannin duniya .

“A fannin noma, a yau Najeriya na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke sayo abinci daga ƙetare, amma duba da yawan jama’ar ƙasar idan ƙasar ta yi amfani da shawarwarin da ake bai wa manoman ƙasar, to akwai yiwuwar ƙasar za ta samu bunƙasa a fannin samar da abinci, ta yadda ma za ta zama babbar mai fitar a abinci a duniya”, in ji shi.

Hamshaƙain attajirin ya kuma ce ya kamata manoman ƙasar su rungumi hanyoyin noma na zamani tare da amfani da irin shuka mai inganci domin samun bunƙasar noman abinci a ƙasar.

Haka kuma ya yi kira ga gwamnatin ƙasar ta bunƙasa fannin lafiyarta.

“Ya kamata a bai wa fannin lafiya fifiko. Gwamnatin ƙasar ta jima tana yin shirin ɗaukar nauyin fannin lafiyar fiye da yadda yake a yanzu. To sai dai a haƙiƙanin gaskiya a Najeriya ba a biyan haraji yadda ya kamata”.

Bill Gates ya ce duk ‘yan ƙasar da ke son ilimi da lafiyarsu do ya wajaba a kansu su riƙa sauke haƙƙokin da ke kansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Fasinjoji 18 Sun Mutu a Hatsarin Mota Yayin Dawowa Daga LegasGwamnatin Najeriya ta ƙudiri Anyiar Tara N2.5trn Daga Kuɗaɗen Shiga a 2026Wanda ya Kafa PRNigeria ya Nufi Kotu Don Daukaka Kara Kan Watsi da Karar ₦1bn da ya Shigar Kan NIPSSObi ya yi Tsokaci Game da Hukuncin da Kotu ta yi na Soke Rijistar Jam'iyyar NDC Soke Rijistar NDC Murƙushe Dimokuraɗiyya ne - PDPAn Gurfanar da ƙarin Mutane 17 kan Kashe Matar Aure a Jihar KadunaCutar Tamowa: Gwamnatin Kebbi ta Karyata Rahoton MSF Kan Mutuwar ƙananan  Yara a JiharJam'iyyar NDC ta Magantu Bayan Kotu ta Soke Rijistar taAbinda Ke Haddasa Matsalolin Tsaro a Jihar mu - Gwamnan Ahmed Aliyu Babban Bankin Najeriya ya Umarci Bankuna da su Rufe Asusun Mutane da Ake Zargin da Tallafawa Ta'addaci Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta'addaci a Najeriya Mun Ceto Mutane 47 Daga Hannun Mayaƙan ISWAP - Rundunar Sojin NajeriyaSanatocin za su Fara Duba ƙudirin  Kafa ƴan Sandan Jihohi Ranar Laraba - AkpabioMatakin da Amurka ta ɗauka na Cire Tallafin Cutar HIV a Afirka ta Kudu Zai Janyo Asarar Rayuka - MDDAn Gurfanar da Mutane 24 Bisa Zargin Kashe Matar Aure a Maraban Jos
X whatsapp