Home AFIRKA Mahukuntan Chadi sun sabunta gargaɗi kan yiwuwar sake fuskantar ambaliya

Mahukuntan Chadi sun sabunta gargaɗi kan yiwuwar sake fuskantar ambaliya

Mahukuntan Chadi sun fitar da sanarwar gargaɗi da ke buƙatar jama’a su ɗauki matakan kariya da kuma yin taka-tsan-tsan don kaucewa asarar rayuka bayan ambaliyar da ta sake kunno kai a tsakar birnin N’Djamena sakamakon mamakon ruwan sama da kuma tumbatsar kogin Chari.

A ɓangare guda bayanai sun ce kogin Logone ya yi tumbatsa mafi ƙololuwa da ba a ga irinta cikin shekaru 30 zuwa 40 da suka gabata ba, wanda ya sanya matakin da ya sanya fargabar sake tsanantar ambaliyar ƙasar wadda kawo yanzu ta hallaka mutane 576 tare da raba wasu miliyan 1 da dubu 900 da matsugunansu tun bayan farowarta a watan Yulin da ya gabata.

Masana sun yi gargaɗin cewa wasu sassa na Chadi ka iya fuskantar zabtarewar laka ƙari kan ambaliyar da ake ci gaba da gani tsawon makwanni.

Ƙasashe da dama a yankunan yammaci da tsakiyar Afrika ne suka yi fam ada ambaliyar ruwa a damunar bana, sai dai halin da ake ciki a Chadi ya fi ko’ina tsananta lura da yadda matsalar ta shafi miliyoyin iyalai.

Shugabar hukumar kula da albarkatun ruwa ta Chadi Sakine Youssouf ta ce tumbatsar kogin Logone ya wuce yadda ake tsammani inda a jiya Laraba ya kai mita 8.18 fiye da yadda aka yi tsammanin tumbatsar shi.

Tuni dai Firaminista Maye Halina ya jagoranci wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki don ɗaukar matakan da za su baiwa jama’a kariya daga ƙaƙƙarfar ambaliyar da ake hasashe da kuma wadda tuni ta shafi yankuna 17 cikin 23 da ƙasar ke da su ciki har da fadar gwamnati.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp