Home SIYASA Jam’iyyar ADC ta Kori Nafi’u Bala Gombe

Jam’iyyar ADC ta Kori Nafi’u Bala Gombe

Nafi'u Bala Gombe

Jam’iyyar ADC ta Kori Nafi’u Bala Gombe

 

Jam’iyyar adawa ta ADC ta kori tsohon maitaimakin jam’iyyar na ƙasa mai iƙirarin shugabancin Jam’iyyar Nafi’u Bala Gombe da wani mamba na jam’iyyar Leke Abejide. Jam’iyyar ta sanar da hakan ne a yayin taronta na ƙasa da ta gudanar.

An kori Nafi’u Gombe ne dalilin “yi wa jam’iyya zagon ƙasa”, kamar yadda Faisal Kabiru ɗaya daga cikin masu magana da jam’iyyar ya shaida wa BBC Hausa, wanda hakan ya jefe jam’iyyar cikin mawuyacin hali.

An kori nafi’u Gombe tare da wasu da suka haɗa da Kenneth Ehiator daga Abia wanda shi ma yake iƙirarin shugabancin jam’iyya a jihar, da Stella Chukwu da kuma Elias Adiukwu.

Nafi’u da ya dage kan zama shugaban jam’iyyar ya fitar da sanarwar waɗanda suka shiga jam’iyyar su Sanata Rabi’u Musa Kwankwanso ba halastattun ‘yan jam’iyya ba ne, saboda sun shiga ba ta hannunsa ba, kazalika katin ‘yan jam’iyyarsu a shi da wani amfani.

Ya kuma jagoranci zanga-zangar da aka yi a Abuja, wadda ta mayar da hankali wajen neman hukumar zaɓe INEC ta yarda da shi a matsayin halastaccen shugaban ADC.

 

`

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp