Kungiyar UKCCSG ta Nuna Rashin Jindadin ta Kan Yajin Aikin ‘Yan Adaidaita Sahu a Jahar Kano

Abike Dabiri CEO NIDCOM
Abike Dabiri CEO NIDCOM

Kungiyar UKCCSG ta Nuna Rashin Jindadin ta Kan Yajin Aikin ‘Yan Adaidaita Sahu a Jahar Kano

Inuwar kungiyoyi masu zaman kansu ta jihar kano, Mai labin Umbrella of kano concern civil Society groups, ta bukaci gwamnan jihar kano dr. Abdullahi Umar Ganduje daya sanya bakin cikin dambarawar dake faruwa tsakanin hukumar karota da matuka baburan Adaidaita sahu a jihar kano.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Comrade Ibrahim Ali wadda aka raba manema labarai a yammacin Talata.

Sanarwa tace kungiyar ta lura da yadda al’ummar jihar kano suka shiga cikin mawuyacin hali sakamakon yajin aikin da kungiyoyin matuka baburan Adaidaita sahun suka tafi.

Yajin aiki da yayi sanadiyar dakatar da al’amaru da dama wanda ya hadar da dakatar da daliban makarantun sakandire, na Primary hadi da na kwalejoji da jami’oin jihar kano zuwa makarantun su.

Kungiyoyin suka ce matsayin su na kungiyoyin fararen hula, suna jajantawa Al’ummar jihar kano bisa wannan mataki da masu tuka baburan Adaidaita sahun suka dauka.

Sannan kuma suna kira ga gwamnan jihar jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje daya sanya baki cikin wannan lamari, sannan yayi kira ga shugaban cin hukumar karota.

Kungiyar tace ta san gwamnatin jihar kano nada kyawawan manufofi, amma suna ganin kaar da gangan shugaban hukumar ta Karota ke yiwa gwamantin zagwan kasa ta hanyar furta kalamai masara dadi ga ‘ya’ayn kugiyar dake kukan hukumar na tsawwala musu wajen karabar haraji da sanya musu tara babu gaira babu dalili.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 14 hours 52 minutes 20 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 33 minutes 45 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here