Shugaba Buhari ya Nada Sabon Shugaban HYPREP

Shugaba Buhari ya Nada Sabon Shugaban HYPREP

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin jami’in da zai shugabanci aikin HYPREP.

Giadom Ferdinand Dumbari zai rike shugabancin HYPREP tun daga yanzu har zuwa shekarar 2026.

Dr. Giadom Dumbari kwararre ne a bangaren ma’adanai, kuma babban malami ne a jami’ar UNIPORT.

FCT, Abuja – Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Giadom Ferdinand Dumbari a matsayin wanda zai kula da aikin HYPREP.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin ma’aikatar muhalli na tarayya a ranar Talata, 8 ga watan Maris 2022. Jaridar nan ta The Cable ta fitar da wannan rahoton.

Dr. Giadom Ferdinand Dumbari zai shafe shekaru hudu yana wannan aiki na magance illar gurbacewar wuri da ake samu a dalilin sinadaran ‘Hydrocarbons’.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, Ferdinand Dumbari ya samu Digirin farko a ilmin ma’adanan kasa a jami’ar Fatakwal da M. Phil a jami’ar jiha duk a Ribas din.

A wannan jami’ar tarayya da ke Fatakwal ne Giadom Ferdinand Dumbari ya yi PhD a fannin ma’adanai. Malamin jami’ar ya yi rubuce kusan 30 a bangarensa.

Masani a wannan harka

Sabon shugaban na HYPREP ya shafe sama da shekaru 20 yana nazari da bincike a kan hadarin wadannan ‘Hydrocarbons’ da manyan karafuna da sauran sinadarai.

A ciken irin nazarin da Ferdinand Dumbari ya yi, ya duba yadda sinadaran suke gurbata Ruwan kasa. Legit.ng ta fahimci hakan ta sa yake ba UNEP shawara tun 2019.

Jaridar Independent ta ce kafin wannan nadin mukami da aka ba shi, Dr. Ferdinand Dumbari kwararren ma’aikaci ne da yake aiki da UNEP a yankin Ogoniland.

Bugu da kari, Dr. Dumbari yana cikin kungiyoyin kwararrun masana a kan harkar ma’adanai na kasa. Sannan ya yi aiki da gwamnatin Ribas, NDDC, da kamfanin NDPD.

Ya cancanci ya rike HYPREP

Mun samu labari cewa shugaban na HYPREP ya rike mataimakin shugaba na aikin Shell PER DEC COY, don haka wani abokin aikinsa ya ce lallai ya cancanta.

Wannan jami’in NSCDC da ya yi aiki da shi a Fatakwal ya ce shakka babu Dr. Dumbari ya dace da wannan mukami domin kuwa an dauko wanda ya san bakin zaren.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 19 hours 49 minutes 1 second,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 30 minutes 26 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here