Home SIYASA Shugaba Buhari Zai Gana da Jiga-Jigan Sanatocin APC a Abuja

Shugaba Buhari Zai Gana da Jiga-Jigan Sanatocin APC a Abuja

Shugaba Buhari Zai Gana da Jiga-Jigan Sanatocin APC a Abuja

Bayan ganawa da gwamnonin jam’iyyar APC, shugaba Buhari zai gana da jiga-jigan sanatocin APC a Abuja.

Rahoton da muka samo daga majiya ya bayyana cewa, za su yi zaman ne da misalin karfe 12 na rana.

Shugaban ya gana gwamnoni a baya, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi taron gangamin APC.

FCT, Abuja – Jiga-jigan jami’an majalisar dattawa da aka zaba a karkashin inuwa jam’iyyar APC a yau za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa ta Villa da ke Abuja.

Jaridar Daily Sun ta tattaro cewa ana sa ran sanatocin za su isa Cibiyar Taro na Gidan Gwamnati da karfe 11:30 na safe don gwajin Korona kafin daga bisani su shiga ganawa da shugaban a daidai karfe 12:30 na rana.

Tun dawowar shugaban kasa daga birnin Landan inda yaje jinya, shugaban ya gana da tawagar gwamnoni da jiga-jigan jam’iyyar APC.

A wannan karo, shugaban zai gana da sanatoci. Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san dalilin ganawar tasu ba, amma ana kyautata zaton batu ne da ya shafi taron gangamin APC.

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa kan harkokin da suka shafi yada labarai ya bayyana ganawar Buhari da shugabannin majalisar.

A cewarsa:

“Bayan ganawa da mambobin kungiyar gwamnonin APC da masu neman shugabancin jam’iyyar APC a jiya, shugaban kasa @MBuhari a yammacin yau ya yi irin wannan ganawa da shugabannin jam’iyyar APC a majalisar dokokin kasar.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp