Hukumar NITDA ta Fara ba da Horo ga Mutane 200 Ƴan Gudun Hijira a Abuja
A ƙoƙarinta na cimma fata da burin mai girma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, (GCFR), na fidda ƴan Nageriya kimanin mutum miliyan ɗari daga cikin ƙangin fatara gami da talauci, hukukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), ƙarƙashin jagorancin Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), ta ƙaddamar da shirinta na ba da horon ƙwarewa kan fasahar zamani ga ƴan gudun hijira, matafiya, da kuma waɗanda fitintinu su ka raba su da muhallansu.
Read Also:
Horon wanda za a shafe tsawon yini (5) ana gudanar da shi, an ƙaddamar da fara shi ne a yau a cibiyar horar da ma’aikata ilimin aikin gwamnati a zamanance, (E-Government Training Center), da ke yankin Kubuwa, birnin tarayya Abuja, kana haɗin gwiwa ne a tsakanin hukumar ta (NITDA) da kuma hukumar kula da al’amuran ƴan gudun hijira ta tarayyar Nageriya, “National Commission For Refugees Migrants And Internally Displaced Persons (NCFRMI).
Horon da ke da manufar bunƙasa ƙwarewa kan hikimomi da dabarun ilimin fasahar sadarwar zamani domin harkar kasuwanci da sana’o’in dogaro da kai a zamanance, kimanin mutane ɗari biyu ƴan gudun hijira, da masu ƙaura, da waɗanda iftila’i ya raba da muhallansu ne za su amfana a birnin Abuja kafin daga bisani kuma a faɗaɗa shirin zuwa sauran Jihohin Nageriya.
Mai girma shugaban ƙasa Malam Muhammadu Buhari, (GCFR), tuntuni ya yi alƙawarin fidda ƴan Nageriya kimanin mutum (Miliyan 100) daga cikin talauci nan da shekarar (2030) da yardar Allah. Wanda a ƙarƙashin wannan turba hukumar ta (NITDA), da ma’aikatar sadarwa, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), su ka himmatu ka’in da na’in wajen ba wa al’ummar Nageriya daban-daban horo kan hikimomi da dabaru na ilimin fasahar sadarwar zamani domin su samu sana’o’i da kasuwancin dogaro da kai.
Litinin, 14 ga watan Fabarairu, 2022.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 39 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 21 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com