Na Amince na Sasanta da Rasha a Iyakar Ukraine da Belarus – Shugaban Ukraine
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelinsky ya ce ya amince ya sasanta da Rasha a wani wuri kan iyakar Ukraine da Belarus
Mista Zelensky ya ce a tattaunawar da ya yi da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, Ukraine ta amince ta gana da Rasha ba tare da wani sharaɗi ba a kan iyakar Ukraine da Belarus a kusa da kogin Pripyat.
Read Also:
Shugaban Ukraine ya ce Mista Lukashenko ya ce ya ɗauki alhakin tabbatar da dakatar da shawagin dukkanin jiragen sama, masu saukar angulu da masu kakkabo makamai mai linzame lokacin ziyarar domin tattaunawar tsakanin ɓangarorin biyu.
Tun da farko Msita Zelensky ya yi watsi da tayin Rasha na hawa teburin tattaunawa da Belarus. Ya ce ya fi buƙatar a tattauna a wata ƙasa saɓanin Belarus.
Belarus babbar aminiyar Rasha ce a yaƙin da take da Ukrainer.
Rasha ta sanar a ranar Lahadi cewa ta tura wakilai Belarus domin tattaunawa da jami’an Ukraine.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 17 hours 14 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 55 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com