Kocin Najeriya Augustine Eguavoen na Fatan Dawo da Victor Moses
Mai horas da tawagar Super Eagles Augustine Eguavoen na son janyo hankalin tsohon dan wasan Chelsea Victor Moses ya koma bugawa kasarsa da za ta halarci Qatar 2022.
Dan wasan mai shekara 31 da ke taka leda a kungiyar Spartak Moscow da ke Rasha, ya ajiye takalmansa ne a 2018.
Shugaban Hukumar Kwallom Kafa ta Najeriya (NFF) Amaju Pinnick da tsohon kocin Najeriya Gernot Rohr duka sun yi kokarin dawo da dan wasan amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Sai dai Eguavoen, wanda ya gaji Rohr a watan Disamba ya ce: “muna son kasarmu ta yi abin arziki.
Read Also:
“Ina son kwallon Victor Moses kuma ina ta kokarin dawo da shi ya ci gaba da bugawa kasarmu.
“Baya cikin tawagarmu da za ta kara da Ghana domin neman gurbi a gasar cin kofin duniya, amma muna sa ran ganinsa a gaba saboda muna son kasar ta yi abin arziki.
“Ko kana so ko baka so yana da gudunmuwar da zai iya bayarwa. Amma a yanzu yana wasa a Rasha, kuma mun san duk matsalar da take faruwa tsakanin Rasha da Ukrain. Cikin farin ina sanar da cewa tattaunawarmu da shi ta fara nisa.”
Moses ya koma Spartak daga Chelsea a 2021, sai dai zai iya sauya kungiya a makonni masu zuwa
Fifa ta shaida wa duk wasu ‘yan wasa da ke taka leda a Rasha su dakatar da kwataraginsu da kasar su kuma fice cikin kankanin lokaci.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 6 hours 47 minutes 31 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 8 hours 28 minutes 56 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com