Home SIYASA Ma’aikatar Bada Agaji ta Kafa Cibiyoyi Takwas Domin Kula da Wadanda su...

Ma’aikatar Bada Agaji ta Kafa Cibiyoyi Takwas Domin Kula da Wadanda su ke Sansanin Gudun Hijira a Garuruwan Zamfara – Kwamishinan Jahar

Ma’aikatar Bada Agaji ta Kafa Cibiyoyi Takwas Domin Kula da Wadanda su ke Sansanin Gudun Hijira a Garuruwan Zamfara – Kwamishinan Jahar

 

Gwamatin Zamfara ta na dawainiya da mutane fiye da 700, 000 da matsalar rashin tsaro ta shafe su.

Ibrahim Magaji Dosara wanda shi ne Kwamishinan yada labaran Zamfara ne ya bayyana wannan.

Kwamishinan tsaro ya ce gwamnatin Muhammad Bello Matawalle ta dauki ‘yan banga har 4200 aiki.

Kaduna – gwamnatin jihar Zamfara ta ce ma’aikatar bada agaji ta kafa cibiyoyi takwas domin kula da wadanda su ke sansanin gudun hijira a garuruwan jihar.

Daily Trust ta rahoto gwamnatin ta na cewa akwai sama da mutane 700, 000 da ke gudun hijira.

Kwamishinan yada labarai na Zamfara, Ibrahim Magaji Dosara ya shaidawa manema labarai a Kaduna cewa gwamnati na dawainiya da masu gudun hijira.

Alhaji Ibrahim Magaji Dosara ya ce a kowace karamar hukuma da ke jihar Zamfara, akwai jami’an bada agaji na gaggawa da aka samar domin su bada taimako.

Wadannan jami’ai za su rika bada tallafi ga wadanda matsalar tsaro ta shafa a kowace karamar hukuma.Akwai kananan hukumomi 14 ne a jihar ta Zamfara.

“Baya ga rabon kayan abinci, katifa, gado, tufafi da sauransu da gwamnatin jiha ta ke yi, ma’aikatar ta na yabon kokarin da kungiyoyin kasashen waje ke yi.”

“Wadannan kungiyoyi su na karfafawa gwamnatin jihar ta hanyar bada kudi ga masu gudun hijira, ana raba N30000 zuwa N40000 ga wadanda abin ya shafa.”

“Gwamnatin tarayya ta narka makudan kudi a kan haka Gwamnatin Zamfara ta na godewa duk wadanda suka taimaka wajen yaye wa mutanenta bakin ciki.” – Alhaji Ibrahim Magaji Dosara

An rahoto kwamishinan yana cewa ana horas da wadanda ‘yan bindiga suka fatattaka.Ana koya masu tukin keke napep, tela, hada ruwa, wanzaci da sauransu.

An dauki ‘yan sa-kai Kwamishinan tsaro da harkokin gida, Mamman Ibrahim Tsafe ya ce sun dauki ma’aikatan sa-kai 4200 aikin banga domin su kare jama’a daga ta’adin ‘yan bindiga.

DIG Mamman Tsafe ya ce an koyawa ma’aikatan rike makami domin su taimakawa jamii’an tsaro.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp