‘Yan Bindiga Sun Sake Hallaka Dandazon Mutane a Kaduna, Zamfara da Neja
A kalla mutum sama da 40 ne ‘yan bindiga suka harbe a wani hari a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Maharan sun kai hare-haren ne a garuruwa daban-daban na ƙaramar hukumar Giwan.
Wannan na zuwa ne bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a filin jirgin sama na Kaduna a ranar Asabar ɗin da ta wuce, inda suka kashe a ƙalla ma’aikata biyu na filin jirgin.
A yanzu haka hare-haren da ake yawan kai wa jihohin Zamfara da Neja masu maƙwabtaka da Kadunan sun sa mutune barin garuruwansu.
Tunin aka yi jana’izar waɗanda aka kashe ɗin a wasu garuruwan na yankin Giwan amma har yanzu a wani garin ba a yi zana’izar mutanen da suka mutu ba.
Wani magidanci daga garin Tsaunin-Mayau da yanzu haka ke gudun hijira a wani garin bayan ya ƙetare rijiya da baya ya yi wa BBC ƙarin bayani.
“Kashe mu suke yi kamar suna kashe kiyashi. Da ƙarfe hudu na yamma suka dirar mana, a ƙalla ba a ƙasara ba sun zo da babur ya kai 300.
“Sun kashe mutum 14 nan take a gidana, gawarwakin ma suna nan ba a kwashe su ba, ba a yi jana’izarsu ba.
“Ba a yi jana’ziarsu ba don kowa ya gudu ana tsoron cewa za su dawo su sake kashe mutane, duk garin ya tarwatse.
“Tsaknain garuruwan nan uku akwai mutum sun fi dubu ɗaya tsakanin mata da maza da yara. Hanyar cike take da ɗan adam, suna nan kowa a ƙafa yake tafiya.”
Read Also:
Wani zai yi mamaki ko ina jami’an tsaro suke a wannan lokacin?
Shaidan ya ce “wa yake maganar jami’an tsaro, kowa ta kansa yake. Ni kaina babur ya fi 50 da suka kewaye gidana.
“Haka suka fito da ni suka ce ina wayata? Na ɗauka na ba su. Suka ce ina kuɗi? Na ce ba ni da kuɗi.
“Suka sake tambayata ina makami? Na ce musu ba ni da shi. Haka suka yi ta min tambayoyi, da kamar za su harbe ni sai kuma Allah Ya taimake ni dai ba su harbe ni ba,” in ji shi.
Amma ya ce ya san Allah ne Ya kuɓutar da shi ba wai don ya fi ƙarfinsu ko dabararsa ba.
Abin da ya faru a Zamfara da Neja kuma?
A jihar Zamfara ma mata da yara ‘yan gudun hijira ne daga garin Ruwan-Gizzau suka yi gudun hijira garin Jangebe bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai a ranar Lahadi, kamar yadda wata mata ta shaida wa BBC.
Can a jihar Neja ma an kai hare-hare a ƙaramar hukumar Munya a garuruwa da dama kamar yadda wannan mazaunin yankin ke cewa.
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin hukumomin tsaro daga jihohin da abin ya faru, amma hakan ya ci tura.
Sai dai a jihar Zamfara hukumar ‘yan sanda ta tabbatar mana da faruwar lamarin inda ta ce gida biyu ne maharan suka ƙona tare da kashe mutum biyu.
Hukumar ta kuma ce jami’an tsaro ne suka tare su sai suka nufi wannan gari, kuma zuwa yanzu an tura ƙarin jami’na tsaro a yankin.
A yanzu dai al’ummomi mazauna karkara na koka wa da yawaitar kai hare-hare a waɗannan jihohi, a yayin da hukumomin ke cewa suna ci gaba da yin bakin ƙoƙarinsu wajen ɗaukar matakan da suka dace game da lamarin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 11 hours 52 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 33 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com