• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home Taska Fusatattun Matasa sun Kai Hari a Matsugunin Fulani
  • Taska

Fusatattun Matasa sun Kai Hari a Matsugunin Fulani

By
Prnigeria
-
April 11, 2022
Arewa Award

Fusatattun Matasa sun Kai Hari a Matsugunin Fulani

‘Yan bindiga da ba’a san ko suwaye ba sun hallaka sabon shugaban Al’ummar Kakura dake Karamar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna a ranar Lahadi Isiaku Madaki.

Jaridar Emergency Digest ta rawaito Wani mazaunin yankin Baban David ya bayyana cewa an nada marigayin matsayin shugaban Al’ummar ne a ranar Asabar.

“Mun taru a gidansa da sanyin safiyar ranar ta Asabar domin taya shi murnar nadin da aka yi masa, amma munyi mamakin yadda muka fara jin karara harbe-harbe a safiyar ranar Lahadi.

“Karar habin ta razana mu matuka, domin yadda muka ji karar ta hana mu fitowa daga gidajen mu, sai dai daga bisani aka fada mana ‘Yan Bindigar sun halaka shi a gaban matar sa da ‘Ya’yan sa.

Read Also:

  • Dalilin Tinubu na soke afuwar da Ya yiwa Maryam Sanda
  • Gwamnan Jihar Katsina ya samar sabuwar ma’aikata a jihar
  • Za’a samar da sabbin jihohi 6 a Nijeriya

“Mun sami gawar sa yashe akar; Matar sa ta fada mana ‘Yan Bindigar sun karya kofar gidan suka kuma hallaka mijin nata ta hanyar harbi, amma dai basu dauki komai ba, kuma ba suyi garkuwa da kowa ba.

Sai dai wani rahoto ya bayyana cewa a safiyar wannan rana, wasu fusatattun matasa sun kai hari a matsugunin Fulani inda ake fargabar mutuwar mutane 14.

Wani bafullatani dake zaune a yankin, Malam Buhari ya bayyana cewa, ‘Yan Asalin yankin sun kewaye matsugunan su inda suke cewa su bar musu yankin tunda sun fara munafurtar su.

Ya kara da cewa yayin da suke fita daga yankin an kai musu farmaki tare da kashe wasu daga cikin su, yana mai cewa “ akan hanyarmu ta zuwa kauyen mun kirga gawarwaki hudu, daga bisani kuma a cikin daji mun kirga gawarwaki wasu mutum 10.

A yayin hada wannan rahoton an tura ‘yan sanda zuwa garin domin maido da zaman lafiya, duk da cewa yanzu haka Al-amura sun fara komawa yadda suke a baya, duk da cewa akasarin mutane yankin sun tsere saboda fargaba.

Sai dai kawo yanzu rundunar ‘yan sandan jihar, da gwamnatin jihar basu ce komai ba dangane da lamarin.

By PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
  • TAGS
  • 'yan bindiga
  • Emergency Digest
  • Fulani
  • kaduna
Previous articleAn Fara Kace Nace Tsakanin Tinubu da Osibanjo
Next article‘Yan Sanda a Jihar Zamfara Sun Sami Nasarar Kubutar da Mutane 39 da Hannun ‘Yan Bindiga
Prnigeria

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Azumin Bara: Talge Muka Riƙa Sha a Hannun Maharan Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Zambar N2.2bn: EFCC ta Sake Gurfanar da ɗan Tsohon Shugaban PDP

Magance Karancin Naira: CBN ya Umarci Bankuna da su yi Aiki a Ranakun Asabar da Lahadi

Hatsarin Mota ya yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 25 a Bauchi

Hukumar NITDA ta Gabatar da Satifiket ga Matan da Suka Samu Horo Kan Fasahar Zamani

Ambaliyar Ruwa a Jigawa: Gidauniyar Ƙasar Qatar da ta Malam Inuwa Sun Raba Tallafin Abinci ga Mutane 1,000

An Gudanar Da Bikin Arewa Stars 30 Under 30 2022, Cikin Nasara

Manomi Yayiwa Wata Mata Yankan Rago

‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi da Kashe ‘Yan Sanda Biyu a Anambra

Gidauniyar Malam Inuwa Da Kokarinta Na Ilmantar Da Mutanen Karkara Da Rugage

Gidauniyar Malam Inuwa ta Ɗauki Nauyin Koyar da Ƴa’yan Fulani Al-ƙur’ani

Bincike: Shin Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta ƙirƙiro da Tambayoyi Domin Tantance kungiyoyin Musulmi da Kirista a kidayar 2023? 

Recent Posts

  • Dalilin Tinubu na soke afuwar da Ya yiwa Maryam Sanda
  • Gwamnan Jihar Katsina ya samar sabuwar ma’aikata a jihar
  • Za’a samar da sabbin jihohi 6 a Nijeriya
  • Jami’ar ABU ta musanta labarin samar da makamin Nukiliya
  • Mayakan Boko Haram sun fara kai hari da jirage marasa matuki a Borno

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1595 days 14 hours 51 minutes 37 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1577 days 16 hours 33 minutes 2 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Dalilin Tinubu na soke afuwar da Ya yiwa Maryam SandaGwamnan Jihar Katsina ya samar sabuwar ma'aikata a jiharZa'a samar da sabbin jihohi 6 a NijeriyaJami'ar ABU ta musanta labarin samar da makamin NukiliyaMayakan Boko Haram sun fara kai hari da jirage marasa matuki a BornoBabu wasu bayanan an yi wa masu bin wani addini kisan ƙare dangi - SultanZa ayi bincike kan masu laifin da Tinubu ya yiwa AfuwaTinubu ya taya Kwankwaso munar cika shekaru 69 a duniyaMajalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da Amupitan a matsayin shugaban INECNAHCON ta bayyana dalilian da suka saka Saudiya rage mata kujerun aikin hajji banaDalilin da ya sa Amnesty ke neman a soke hukuncin kisa a NajeriyaGwamnan jihar Bayelsa, ya fice daga jam'iyyarsa ta PDP.Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta amince da naɗin Joash AmupitanGwamnatin Najeriya ta cire darasin Lissafi cikin sharuɗan samun gurbin karatun Jami'a ga wasu ɗalibanGwamnan Enugu ya koma APC bayan ficewa daga PDP
X whatsapp