Home General Masu Garkuwa Da Suka Yi Garkuwa Da Wata Mata A Legas Sun...

Masu Garkuwa Da Suka Yi Garkuwa Da Wata Mata A Legas Sun Nemi Fansan Miliyan 10

‘Yan bindigar da sukayi garkuwa da wata mata a garin Legas sun tuntubi ‘yan uwan ta, in da suka bukaci a biya su fansar naira Miliyan 10.

An ruwaito cewa masu garkuwar da su kayi badda bami matsayin masu sayen kaya a babban kantin dake unguwar Plywood ta Epe da misalign karfe 10:07Pm sun bayyana cewa suna bukatar sayen ruwa ne kamar yadda mijinta ya bayyana wanda yace suna tare a kantin.

Sai dai ana tsaka da hada-hadar cinikayya a kantin ne kawai hasken lantarki ya dauki abinda ya kai ga ‘yan bindigar sun amshe wayoyin ma’auratan baya ga lakada musu dukan kawo wuka.

Daga bisani kuma suka rufe mijin matar a kantin suka kuma yi awon gaba da matar da nufin yin garkuwa da ita.

Wani dan uwan wadda aka yi garkuwar da ya nemi a sakaye sunan sa, ya bayyana cewa masu garkuwar sun kira mijin matar inda suka bukaci ya biya naira Miliyan 50 matsayn fansar matar sa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bakin kakakin ta SP Hudenyin ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace tana bincike domin tabbatar da an kubutar da matar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp