Danmadami Ya Maye Gurbin Onyeuko A Matsayin Daraktan Yada Labaran DHQ

Shalkwatar tsaron Nijeriya DHQ, ta nada manjo Janar musa Danmadami matsayin sabon Darakata yada labaran ta, DDMO.

Dan madami zai maye gurbin Manjo janar Bernard Onyeuko wanda aka tura zuwa shalkwatar tsaro, sashen kula da dabarun aiki matsayin darakta sayen kayyaki.

Da yake jawabi yayin taron manema labarai na mako biyu-biyu a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, Benard Onyeuko, yace sabon daraktanda aka nada ya yi alkawarin karfafa nasarorin da wanda y agada ya samu.

Dan madami ya kuma yi kira ga wakilan kafafen yada labarai, dasu bashi goyon baya da hadin kan da suka ba wanda y agada, domin samun gagarumar nasara.

“Ina so in roke ku da ku bani goyon baya da hadin kai don na sami damar yin nasara,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com