Home General Dakarun Sojin Nijeriya Sun Halaka Manyan Kwamandojin Kungiyar Boko Haram A Kasar

Dakarun Sojin Nijeriya Sun Halaka Manyan Kwamandojin Kungiyar Boko Haram A Kasar

shalkwatar tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa dakarunta sun kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram cikin makwanni biyu da suka gabata.

A wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, rundunar tsaron ta ce dakarun Operation Hadin Kai ne suka kashe kwamandojin ta hanyar yi musu ruwan bama-bamai a maɓoyarsu.

Hedikwatar tsaron ta ce dakarun sun kuma halaka sama da ‘yan ta’adda 57 a wurare daban-daban bayan samame da suka kai tsakanin ranakun 11 zuwa 25 ga watan Agusta a yankin arewa maso gabashin kasar.

Shugaban sashen harkokin yaɗa labarai na rundunar, Manjo Janar Musa Danmadami, ya bayyana cewa samamen sun kunshi wanda aka yi ta sama da kasa a kan maboyar mayakan na Boko Haram da na ISWAP a jihohin Borno da Yobe.

Danmadami ya ce daya daga cikin kwamandojin da aka kashe shi ne Uzaifa, wanda yake cikin manyan jagororin kungiyar hudu.

Ya kara da cewa an kama mutum takwas da ake zargi na aikata ta’addanci da kuma hudu da ke kai wa ‘yan bindiga makamai, inda aka ceto fararen hula hudu.

A cewarsa, ‘yan Boko Haram aƙalla 1,652 da iyalansu ne suka mika wuya ga dakarun Najeriya a wurare daban-daban a baya-baya nan. Daga cikinsu akwai maza 320 da mata 442, sai kuma yara 890.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp