Home General Ana Fargabar Gini Ya Rufta Kan Mutane Da Dama A Jihar Kano

Ana Fargabar Gini Ya Rufta Kan Mutane Da Dama A Jihar Kano

Rahotanni daga kasuwar sayar da wayoyin hannu dake titin beirut a birnin kano dake Arewacin Nijeriya, na cewa wani bene ya rufta kuma ana tsammanin ya danne mutane da dama.
shaidun gani da ido sun shaidawa wakilan mu cewa, yanzu haka ana cen ana kokarin ceto wadanda ke karkashin baraguzai, yayin da aka garzaya da wadanda suka ji rauni asibiti.
Ko dai a ‘yan tsakanin nan Wani ginin bene mai hawa uku da ake aikin ginisa ya rufta a unguwar Kubwa da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Faduwar ginin dai ya rutsa da mutanen bakwai a ciki inda jami’an biyu daga cikinsu suka mutu yayin da jami’an hukumar kai daukin gaggawa ta Abuja suka samu ceto mutane biyar daga baraguzan ginin.
Ba kasafai aka fiya samun ruftawar gini a jihar ba, duk da cewa dai shaidun gani da ido sun dora alhakin rushewar kan rashin ingancin kayan aikin gini.
Kawo yanzu dai hukumomi a jihar basu ce kamai kan wannan lamarin ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp