Wike da Masu Ruwa da Tsaki na PDP Sun yi Taro

Wike

Wike da Masu Ruwa da Tsaki na PDP Sun yi Taro

 

SIYASA – Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kira taron shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar.

Taron dai shi ne na farko a jihar tun bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa da kuma rikicin da ya biyo bayan sakamakon ta.

Ko da yake ba a iya gano ajandar taron ba, wata majiya ta shaida wa wakilin PUNCH cewa tun bayan abubuwan da suka faru a jam’iyyar a matakin kasa har yanzu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar ba su ji ta bakin gwamnan ba.

Don haka ana sa ran masu ruwa da tsaki za su ji ta bakin gwamnan kai tsaye kan matsayinsa da kuma matakin da za a dauka na gaba dangane da rikicin PDP.

Wadanda ake sa ran a taron sun hada da shugabannin jam’iyyar, ‘yan majalisar zartarwa na jiha, shugabannin kananan hukumomin jam’iyyar da sauran zababbun wasu.

Majiyar ta ce taron mai muhimmanci yana da nasaba da rikicin da ya barke a jam’iyyar a kwanakin baya, domin gwamnan zai yi wa mutanensa bayanin matsayin da tawagarsa ta dauka na ficewa daga majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar.

Wannan na zuwa ne gabanin wani taron manema labarai da aka shirya yi a safiyar Juma’a 23 ga watan Satumba, 2022, wanda Gwamna Wike zai yi jawabi a gidan gwamnati dake Fatakwal.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 27 minutes 19 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 8 minutes 44 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com