Home SIYASA Allah ya yi wa Mai Garin Lokoja Rasuwa

Allah ya yi wa Mai Garin Lokoja Rasuwa

Allah ya yi wa Mai Garin Lokoja Rasuwa

 

LABARIN SIYASA – An bayar da rahoton rasuwar basaraken gargajiyar Lokoja, wanda aka fi sani da Mai Gari na Lokoja, Alhaji Muhammadu Kabiru Makarfi III.

Majiyoyin fadar da dama sun shaidawa SIYASA DIGEST a daren Laraba cewa mai martaba sarkin ya rasu da misalin karfe 4 na yamma.

Wakilinmu ya kuma tattaro cewa basaraken mai shekaru 80 a duniya ya rasu ne a wani asibitin Abuja da ba a bayyana ba.

Mai Gari ya kwashe watanni yana jinya inda aka kai Asibitoci daban-daban a Saudiyya da Masar kafin daga bisani ya kare a Abuja.

Majiyoyin da suka kware a fadar sun kara da cewa za a yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a ranar Alhamis.

Mai Gari ya hau karagar mulki tun 1991. Ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya da jikoki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp