Home General Sojojin Nijeriya Sun Sami Nasarar Hallaka Mayakan ISWAP 19 a Jihar Borno

Sojojin Nijeriya Sun Sami Nasarar Hallaka Mayakan ISWAP 19 a Jihar Borno

Dakarun sojojin Nijeriya sun sami Nasarar hallaka mayakan boko haram tsagin ISWAP guda 19 tare da kame guda 73 a arewa maso gabashin kasar.

Wannan na kunshe ne ta ckin wata takardar sanarwa da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun darakatan yada labaran rundunar sojin Nijeriya Manjo Janar Musa Danmadami,dake dauke da kwanan watan 6 ga watan Oktoban 2022.

Sanarwar tace tsakanin 22 ga watan Satumba zuwa 4 ga watan Oktoban wannan shekara dakarun sojin Operation Hadin kai yayin da suke gudanar da ikin wazan da zaman lafiya a  kauyukan, tsunuka, da kuma biranen dake yakin arewa maso gabashin Nijeriya, dakarun sun gabatar da atisayen fatattakar mayakan a kananan hukumomin Biu, Damboa, kaga, Kukawa da Gubio duk a jihar Borno.

A yayin harin da dakarun sojojin suka kai sun sami nasara kame masu safarar kaya ga mayakan boko haram da na ISWAP, inda suka sami nasarar kwato kayayyaki da suka hadar da buhu 50 na busasshen Kifi, Buhu 2 na Busasshen Nama, sai kuma jarakuna 55 makare da man Fetir, buhu 1 na gwayi, sai buhu 13 na buredi, buhu wake guda 1, katan 5 na Omon wanke, 3 fakiti 3 na Batiri, sai jaka 50 ta maganin sauro, wayoyin salula 10, sai abun hawa guda 4, keke guda 1. Gami da zunzurutun kudi har naira miliyan 2 da dubu dari 479 da dari 740 da (2,479,740.00) gami da wasu kayyakin amfani.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp