Gwamnatin Somalia na samun goyon baya kan fafutukar da ta ke na ganin an janye takunkumin da aka kakaba mata na hana shigar da makamai kasar, inda a baya bayan nan, Habasha ta bi sahun Uganda wajen goyon bayan janye matakin.
A cikin watan Nuwamba ake sa ran kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri’a kan sabunta takunkumin haramta saidawa Somalia makamai, wanda gwamnati ta ce, cire shi zai taimaka mata wajen yakar mayakan ‘yan ta’adda na Al Shebaab.
Read Also:
Goyon bayan da Habasha ta bai wa Somalia, ya zo ne bayan da a watan Yuli, gungun mayakan Al Shebaab suka kutsa cikin iyakarta, a lokacin da su ke gujewa hare-haren sojojin Somalia.
A halin yanzu, shekaru akalla 30 kenan aka shafe takunkuman hana shigar da makaman na aiki kan Somalia, wadanda shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud da Firaministan Habasha Abiy Ahmed suka ce lokaci ya yi da za a janye su, domin ba da damar kaddamar da cikakken yaki kan mayakan Al Shebaab.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 10 hours 57 minutes 2 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 38 minutes 27 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com