Ana kyatata zaton mutane 4153 da suka kamu da cutar kwalara a Nijeriya, cibiyar kula da cututtuka ta kasar ce ta bayyana hakan ta cikin wani rahoto dake nuna halin da ake ciki game da cutar a kasar.
Jihar Borno na da cikin jihohin dake fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar, yayin da ta samu sama da kashi 60 cikin 100 na adadin wadanda ake kyautata zaton sun kamu da ita a watan Satumba shekarar 2022.
Rahoton ya nuna cewa daga cikin mutane 4153 suka kamu da cutar, jihar Borno da ke arewa maso gabas ce ke kan gaba da adadin masu dauke da cutar da mutane 2626.
Read Also:
Rahoton ya nuna cewa an samu karuwar kashi 42 cikin 100 na adadin wadanda suka kamu da cutar a cikin watan da ake nazari a kai idan aka kwatanta da 2428 da aka samu a watan Agusta.
Rahoton ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 2 ga Oktoba, Najeriya ta samu jimillar mutane 10,745 da ake kyautata sun kamu da cutar, da kuma mutuwar mutane 256 a fadin jihohi 31.
Rahoton ya nuna cewa jihohi 11 ne ke da kashi 86 cikin 100 na adadin wadanda suka kamu da cutar, inda Borno ke kan gaba da mutane 3663, sai jihar Yobe mai mutane 1632.
Sauran jihohin sun hada da Katsina da mutane 767, Taraba 675, Kuros Riba 649, Gombe 470, Jigawa 417 da Bauchi da mutane 304.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 15 minutes 30 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 56 minutes 55 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com