An Yiwa ‘Yan Jaridu 117 Kisan Gilla a Bakin Aikinsu daga 2020 zuwa 2021

Hukumar kula da ilimi, kimiyya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta koka da yadda wani bincike ke nuna cewa kaso mai yawa na wadanda ke kashe ‘yan jaridu basa fuskantar hukunci kana bin da suka aikata.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Duniya ke bikin ranar kare hakkin ’yan jaridu, inda ta cikin rahoton da UNESCO ta fitar yau laraba, ta ce matsalar kisan ‘yan jaridu ta kai kololuwa a halin da ake ciki, yayinda kashi 86 na wadanda suka aikata kisan basa fuskantar hukunci.

Gabanin fitar da rahoton na yau, UNESCO a wani taron manema labarai da ta kira kan  barazanar da ‘yan jaridu ke fuskanta a sassan Duniya, ta bukaci daukar matakan baiwa ‘yan jaridun kariya la’akari da sadaukarwar da suke yi.

Rahoton na UNESCO ya ce wajibi daukar matakan gudanar da bincike tare da tabbatar da ganin an hukunta wadanda ke da hannu a cin zarafi ko kuma kisan ‘yan jaridu.

A cewar hukumar, halin da ‘yan jaridu ke ciki musamman a yankunan da ake fama da yaki ko kuma matsalolin tsaro baa bin yadda ba ne kuma ya na bukatar daukar matakan magancewa.

Manufar ranar ta yau na da nufin kare hakkin ‘yan jaridu tare da kawo karshen tsangwama ko kyara ko kuma cin zarafin da suke fuskanta a bakin aikinsu lamarin da UNESCO ta ce dole a samar da cikakkiyar kariya ga ‘yan jaridar.

Darakta Janar ta hukumar UNESCO Audrey Azoulay ta ce idan har ba a baiwa ‘yan jaridun kariyar da ta kamata ba, kenan za a dankwafar da hakkin fadar albarkacin baki.

Rahoton na UNESCO ya ce tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021 an yiwa ‘yan jaridu 117 kisan gilla lokacin da suke bakin aikinsu, yayinda wasu 91 kuma aka kashe ba a bakin aiki ba.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1188 days 13 hours 27 minutes 54 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1170 days 15 hours 9 minutes 19 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com