Gwamnatin Tarayya Nijeriya ta ce ba wani shiri da take yi na karawa ma’aikatan ta Albashi kamar yadda aka ruwaito a wasu jaridun kasar a kwanakin baya, inda ta ce wasu “alawus-alawus na musamman” ne kawai take shirin karawa.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Olajide Oshundun ya fitar, inda ya jaddada cewa babu batun sake yiwa ma’aikata karin Albashi.
Read Also:
Ngige, yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati a ranar Talata, ya ce kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan albashin ma’aikata na yin nazari, kuma ana sa ran zai fito da tsarin daidaita albashin a sabuwar shekara.
Sai dai ministan a ranar Juma’ar nan ya ce karin da ya yi magana a kai shi kan alawus din wasu ma’aikatan na musamman ba wai karin Albashi ba, inda ya kara da cewa har yanzu ana kan aiki.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kwamitin shugaban kasa kan albashi (PCS) ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya (OSGF) ya karbi shawarwarin duba alawus-alawus na ma’aikatu da hukumomin gwamnati da dama.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 20 hours 35 minutes 41 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 22 hours 17 minutes 6 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com