Home General Tunubu alkawarin bunkasa tsaro da harkokin tattalin arzikin jihar kano idan ya...

Tunubu alkawarin bunkasa tsaro da harkokin tattalin arzikin jihar kano idan ya sami nasara

Dan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya yi alkawarin bunkasa tsaro da harkokin tattalin arzikin jihar kano idan ya sami nasara.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da malaman Arewa maso yammacin Nigeria a jihar Kano.

Yace kasancewar kano cibiyar Arewacin Nigeria akwai bukatar a bata kulawa ta musamman saboda idan ta bunkasa dukkanin jihohin Arewacin Nigeria sun bunkasa.

Bola Tinubu ya kuma yi alkawarin samar da wani tsari da zai taimaka wajen inganta harkokin karatun al-qur’ani saboda magance matsalar barace-barace a kasar.

Ya kuma yi alkawarin baiwa malamai dama a gwamnatin tarayya ta yadda za’a dama da su domin inganta kasar. Tinubu ya bukaci Malamai da su umarci dalibansu da sauran magoya bayansu da su zabe shi saboda yafi dukkanin yan takarar shugaban kasa chanchanta.

Da yake nasa jawabin gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ƙalubalanci masu ganin baiken jam’iyyar APC don ta haɗa yan takarar shugaban kasa duk Musulmi, Inda yace haɗa Musulmi da Musulmi a takarar shugaban kasa ba sabon Abu bane a Ƙasar Nijeriyar .

Ganduje ya kuma bada tabbacin cewa al’ummar Nigeria suna son jam’iyyar APC da yan takarar su Kuma zasu zabe su a babban zaben Mai zuwa .

Malamai da dama ne dai suka halarci taron ganawar  wadanda suka fito daga jihohin Arewacin Nigeria domin halartar taron wanda ke cikin jerin tarukan da aka tsara don yakin neman zaben Tinubu a kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp