Home General Bola Tunibu ya kai ziyarar neman addu’a Fadar Kano.

Bola Tunibu ya kai ziyarar neman addu’a Fadar Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya bukaci  al’ummar jihar da su ci gaba da mutunta shugabanni, sannan su yi amfani da kuri’unsu wajen zaben shugabanni na gari a lokacin zabe .

Sarkin ya bayyana haka ne a yayi da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Apc, Asiwaju Bola Ahmad tunibu a fadar sa dake jihar kano a Arewa maso yammacin Nijeriya.

Cikin sanarwar da sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikewa manema labarai yace Sarkin wanda ya bayyana Kano a matsayin cibiyar harkokin zabe ya yi kira ga jama’a da su yi amfani da kwarewarsu wajen zaben wadanda za su inganta rayuwar al’umma gaba daya.

Tun da farko dan takarar shugaban kasa Bola Ahmad Tunibu ya ce ya zo jihar Kano ne domin kaddamar da yakin neman zabensa a Arewa maso Yamma kuma ya nemi addu’ar Sarkin da kuma al’ummar jihar.

A yayin ziyarar dan takarar shugaban kasa ya samu rakiyar gwamnan jihar Dr. Abdullahi umar Ganduje, da mataimakinsa Dr. Nasiru yusif Gawuna, gwamnan jihar Zamfara, Sanata Barau Jibrin, shugaban jam’iyyar na jiha Abdullahi Abbas, tsofaffin gwamnoni, da manyan jami’an gwamnatin tarayya.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp