Home General ‘yan Bindiga sun sake sace dalibai a jihar Zamfara

‘yan Bindiga sun sake sace dalibai a jihar Zamfara

‘Yan ta’adda a Najeriya sun kai hari kan dalibai mata na Kwalejin Lafiya da ke jihar Zamfara inda suka kwashe guda 4 bayan halartar wani bikin aure.

Bayanai daga yankin sun ce ‘yan ta’addar sun kama wadannan dalibai ne lokacin da suke komawa Kaura-Namoda daga Birnin Magaji bayan tare motocin da ke dauke da su inda suka kwashi matafiya 18, cikinsu har da daliban mata 4 da wasu ‘yan mata 3 da kuma wani mutum guda.

Tuni hukumomin Kwalejin Kula da Lafiyar ta hannun shugaban su Yusuf Maradun ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya ce ba’a cikin makarantar aka kwashi daliban ba.

Maradun ya ce lokacin da aka sace wadannan daliban makarantar na hutun karshen shekara.

Wani ‘dan uwan daya daga cikin daliban ya ce ‘yan ta’addar sun bukaci diyyar Naira miliyan 20 kafin sakin diyarsu.

Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro musamman hare- hare da kuma garkuwa da jama’a domin karbar kudin fansa.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp