Majalisar Dokokin Nijeriya ta Gayyaci shuwagabannin Bankuna Kasar

Majalisar Dokokin Najeriya ta gayyaci shugabannin bankunan kasuwanci domin bayyana a gabanta a ranar Laraba kan karancin sabbin takardun kuɗi da ake fuskanta.
Babban Darakta kuma Shugaban kwamitin Bankunan na majalisar wakilai za su haɗu da kwamitin wucin gadi na Majalisar wanda shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Ado-Doguwa ke jagoranta domin tattauna wannan batu.
A wani zama da majalisar ta yi a ranar Talata, ta yanke shawarar gayyato bankunan domin su zo gabanta su yi bayani kan matsalolin ƙarancin kuɗi da ake samu daga Babban Bankin Najeriya, inda daga baya za ta gayyato shugabannin na CBN domin zuwa amsa tambayoyi.
Majalisar ta kuma bukaci a tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun kuɗi da watanni shida nan gaba.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1255 days 7 hours 52 minutes 2 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 9 hours 33 minutes 27 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com