Home General NNPP tayi Alla-wadai da harin da ‘yan daba su kai gidan Muhy...

NNPP tayi Alla-wadai da harin da ‘yan daba su kai gidan Muhy Magaji

Babbar jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar Kano ta yi Allah wadai da harin da ake zargin wasu yan jam’iyyar APC sun kai gidan Barr. Muhuyi Magaji dake Rimingado da kuma wasu yan jam’iyyar NNPP mazauna garin a daren jiya talata.
‘Yan daba da ake kyautata zaton gwamnatin APC ce ta daukI nauyinsu sun farwa al’ummar da misalin karfe 7:00 na dare bayan da tawagar yakin neman zaben jam’iyyar NNPP suka gama taronsu a garin na Rimingado .
Jam’iyyar NNPP ta jajanta wa al’ummar yankin kan lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutane da dama da kuma barnata kadarorin al’ummar garin, Kuma NNPP ta zargin hakan wani yunkuri ne da APC ke yi na tsoratar da al’umma masu kada kuri’a a zaben dake tafe .
A cikin wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, babban mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben NNPP na kano ya fitar, ya bayyana harin a matsayin na abun da baj dace ba, da Kuma rashin mutunta mutanen Rimingado.
Sanusi Bature ya kara da cewa babu wani matsin lamba da zai hana jam’iyyar NNPP ta dauki matakin da ya dace na cin zarafin ‘yan kasa, wanda kamata yayi jami’an gwamnati su maida hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
“Mun yi sa’a, ‘yan sanda sun kama daya daga cikin wadanda suka kai harin, kuma wanda aka kama shi ne ya raunata guda cikin yan sandan dake aiki a Rimingado.”
Kakakin ya kuma ce, NNPP za ta tabbatar da cewa an yi adalci ga wadanda abin ya shafa tare da gurfanar da wadanda ake zargin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp