Home General Buhari ya yabawa Ganduje bisa asibitin Masu fama da cutar daji a...

Buhari ya yabawa Ganduje bisa asibitin Masu fama da cutar daji a jihar Kano

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje bisa Samar da asibitin Masu fama da cutar daji a jihar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya.
Buhari ya bayyana haka  ne lokacin da yake bude asibitin dake unguwar giginyu a karamar hukumar Nasarawa ta jihar kano.
Buhari yace dole a ya yabawa hangen nesa na gwamna Ganduje na samar da Asibitin Saboda yadda zai taimaka wajen magance fita waje domin neman lafiya da Kuma bunkasa tattalin arzikin Nigeria.
A nasa jawabin gwamnan jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce an samar da Asibitin ne don rage yawan fita kasashen waje domin neman lafiya.
Yace asibitin shi ne irinsa na farko a Nigeria da Africa baki daya, Kuma zai bunkasa tattalin arzikin jihar kano da kasa baki daya.
An dai sanyawa Asibitin sunan Mai dakin gwamnan kano Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje.
Bayan nan Shugaba Buhari ya bude katafariyar Gadar dake Hotoro wacce aka Saka mata sunan Muhammadu Buhari, da gidajen gwamnatin tarayya dake Darmanawa da Kuma Cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Dangote dake kan titin Zaria da dai sauran su.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp