Hukumar ICPC ta kama Manajan Banki da Boye Sabon Kudi

Hukumar yaƙi da laifukan cin hanci da rashawa a Najeriya, ICPC, ta kama manajan ayyuka na reshen bankin FCMB a Jihar Osun saboda zargin ɓoye sababbin takardun naira.

ICPC ta ce ta gano an zuba kuɗi a cikin na’urorin ATM na bankin amma a ɗaɗɗaure ta yadda ba za su iya fita ba idan mutane suka je cira, inda ta yi gargaɗi da a gyara.

“Sai dai da tawagar ta sake kai ziyarar duba a rana ta biyu, sai ta tarar ɗaya daga cikin ATM ɗin na ɗauke da ɗaurarrun kuɗin,” a cewar sanarwar da ICPC ta wallafa a shafukan zumunta.

Bisa wannan dalilin ne kuma jami’an hukumar suka tafi da manajan mai kula da ayyuka, wanda ba ta bayyana sunansa ba, na reshehn bankin na FCMB.

Haka nan, ICPC ta kama wata manajar bankin a Abuja “saboda ƙin saka kuɗi a ATM da gangan ko kuma sabo da mugunta duk da cewa akwai kuɗin,” in ji hukumar.

Jami’an tsaro da suka haɗa da na ‘yan sanda da EFCC na ci gaba da bin sawun bankuna da ɗaiɗaikun mutane don yaƙi da masu ɓoyewa da sayarwa da kuma yaɗa takardun jabu na sababbin kuɗin.

A gefe guda kuma, ‘yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan ƙarancin kuɗin, inda suke shafe awanni a kan dogayen layuka don cirar su a na’urorin ATM.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 16 hours 3 minutes 55 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 45 minutes 20 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com