Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin kwamitin shirye-shiryen mika mulki na ofishin shugaban kasa, wanda zai gabatar da dukkan ayyukan shirin mika mulki ga sabuwar gwamnatin da za ta gaji wannan bayan zaben 2023.
Wannan na cikin wata sanarwa da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar da sa hannun Willie Bassey wanda shi ne daraktan yada labarai a ofishin.
Ga mambobin kwamitin:
1. Sakataren Gwamantin Tarayya – Shugaban kwamitin 2. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya 3. Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma babban sakatare a ma’aikatar shari’a 4.
Manyan sakatarori daga wadannan ma’aikatun gwamnatin tarayya:
Read Also:
- Tsaro
- Harkokin Cikin Gida
- Kudi da Kasafi da Tsare-tsare
- Harkokin Waje
- Yada Labarai da Al’adu
- Babban Birnin Tarayya (FCTA)
- Ayyuka na Musamman
- Ofishin Shugaban Kasa, karkashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya
- Ofishin Ayyukan Yau da Kullum karkashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya
- Ofishin kula da Tattalin Arziki da na Siyasa, karkashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya
- Fadar Shugaban Kasa
5. Ofishin Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro
6. Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya
7. Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya
8. Babban Daraktan Hukumar Tsaro ta NIA
9. Babban Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS
10. Babban Akawun Kotun Kolin Najeriya
11. Wakilai biyu da zababben Shugaban Kasa zai nada
Sakataren Gwamnatin Tarayya ne zai kaddamar da wannan kwamitin ranar Talata 14 ga watan Fabrairun 2023 da karfe 12 na rana a ofishin Sakataren Gwamantin Tarayya.
Baya ga wannan, Sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya sanya hannu kan wata dokar shugaban kasa mai lamba 14 ta 2023 kan Gudarwa da Tafiyar da Ayyukan Kwamitin Mika Mulki na Mukamin Shugaban Kasa.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 22 hours 18 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 23 hours 59 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com