Rundunar sojojin Najeriya ta ce ba za ta lamunci labaran boge da ake yaɗawa da sunan jami’anta ba

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ba za ta lamunci labaran boge da ake yaɗawa da sunan jami’anta ba a shafukan sada zumunta.

Wannan na matsayin wani martani da ta mayar kan wasu rubuce-rubuce da ke yawo a shafukan sada zumunta, ta ce mutanen da ke kokarin haifar da ruɗani ke amfani da sunanta.

Babban Jami’in sadarwa na kasa a rundunar, Brigediya Janar Tukur Gusau, ya ce tuni sun kaddamar da bincike domin hukunta wadanda suka kirkiri wannan labari.

An dai rinƙa yawo da wasu bayanai kan rundunar da ke cewa, wasu daga cikin manyan jami’anta sun gana da daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa domin kawo rudani kan zaben da ake shirin gudanarwa nan da kwanaki goma sha uku masu zuwa.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 17 hours 25 minutes 4 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 6 minutes 29 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com