Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati EFCC ta ce ta kai jami’anta wuraren zaɓe domin sanya ido kan ayyukan zaɓen, ta kuma bayar da lambobin wayar da za a riƙa buga mata domin ko ta kwana.
EFCC ta wallafa haka ne a shafinta na Twitter inda ta bayyana lambobin wayar da za a riƙa kiranta kai tsaye da an ga wani abu mai kama da laifukan kudi a yayin zaɓe.
Read Also:
A wani ɓangare na tabbatar da an yi zaɓukan shugaban ƙasa da na ‘yan majalisa salin alin shi yasa EFCC ta kai ma’aikatan nata.
Tana so ta tabbatar da an yi zaɓen babu cuta babu cutarwa shi yasa za ta sanya ido kan yadda ake sayan kuri’a wani abu da ya zama ruwan dare a siyasar Najeriya, ko kuma bai wa jami’an da ke aiki kuɗi su ɗauke kai a gudanar da wani abu da bai dace ba.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1465 days 22 hours 30 minutes 36 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1448 days 12 minutes 1 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com