Wata gobara ta tashi a kasuwar a Kasuwar Litinin da ke birnin Maiduguri.

Wata gobara ta tashi a kasuwar da ake kira Kasuwar Litinin da ke birnin Maiduguri.

Gobarar, wadda rahotanni suka ce ta tashi ne a daren jiya ta yi ɓarnar da har yanzu ba a tantance ba.

Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar birnin na Maiduguri sanadiyyar gobarar.

Ganau sun tabbatarwa da PRNigeria cewa wutar dai ta tashi da misalin karfe 2 na daren lahadi inda daga bisani ta yadu a sassan kasuwar.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com