Gwamnatin Najeriya ta ce tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ba shi da “wata kimar” da zai nemi a dakatar da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ake yi yanzu haka a ƙasar.
Gwamnatin ta mayar masa da martani ne bayan wasiƙar da ya rubuta a yammacin Litinin, yana mai neman Shugaba Muhammadu Buhari da shugaban hukumar zaɓe Mahmood Yakubu su soke sakamakon wasu yankuna da ya yi zargin cewa na yi maguɗi.
Read Also:
Da yake mayar da martani, Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ya zargi tsohon shugaban da gudanar da zaɓe “mafi muni a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya”.
“Duk da cewa yana bayyana kansa a matsayin dattijo mai kishin ƙasa, an san Obasanjo da goyon bayan wata jam’iyya da kuma yaudarar ‘yan Najeriya ta hanyar tauye musu abin da suka zaɓa,” kamar yadda wata sanarwa daga ma’aikatar yaɗa labarai ta ambato ministan na cewa.
Obasanjo ya ce ba wani sabon abu ba ne a zargi wasu daga cikin ma’aikatan hukumar zaɓen da suka gudanar da aikin da karɓar cin hanci kafin aika sakamako ta hanyar na’ura, abin da ya sa ake zargin an ƙirƙiri wani sakamkon ne.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1244 days 13 hours 5 minutes 15 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1226 days 14 hours 46 minutes 40 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com