Wata kotun majistare a jihar Kano ta aike da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Duguwa zuwa gidan yari bayan gurfanar da shi a gaban kotun.
Ana zargin ɗan majalisar da muggan laifuka ciki har da zargin aikata kisan kai da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba da hannu a kunna wuta a wani gini wadda tayi sanadiyyar mutuwar wasu mutane tare da raunata wasu.
An gurfanar da shi gaban kotu mai lamba 54 dake No man’s land tare da wani mutum wanda ake zargi sun haɗa baki wajen aikata kisan kai da tayar da zaune-tsaye a ƙaramar hukumar Tudun wada da ke jihar ranar Asabar da ta gabata.
Alƙalin kotun ya ɗage shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Maris domin duba buƙatar yiyuwar bayar da belin ɗan majalisar ko kuma akasin haka.
Bayan fitowa daga kotun ne tashar PRNigeria ta sami zarafin tattaunawa da lauyan gwamnatin jihar kano Bar Lamido Abba Soron Dinki inda ya bayyana cewa yanzu haka za su yi Nazari kafin ranar da koton ta sanya a dawo domin cigaba da sauraren karar.
Shima a nasa bangaren lauyan dake kare wanda ake tuhuma Bar. Abdul Adamu Fagge ya bayyana dalilan da ya sanyasu bukatar kotun ta bayar da belin na Alhasan Ado Doguwa.
Akwai lauyoyin masu tarin yawa dake sanya idanu kan Shari’ar a karkashin Barista Mutari Dandago.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1240 days 8 hours 55 minutes 1 second,
Baptist School Students, Kaduna
1222 days 10 hours 36 minutes 26 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com