• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home Taska Azumin Bara: Talge Muka Riƙa Sha a Hannun Maharan Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna
  • Taska

Azumin Bara: Talge Muka Riƙa Sha a Hannun Maharan Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

By
Prnigeria
-
March 29, 2023
Abuja-Khaduna Captives
Arewa Award

Azumin Bara: Talge Muka Riƙa Sha a Hannun Maharan Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

 

Karyewar jari da damfara da miyagun mafarke-mafarke, shan talgen tuwo da gurɓataccen ruwa da kuma murnar shaƙar iskar ‘yanci na cikin abubuwan da har yanzu ke cikin zukatan wasu fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da ‘yan Boko Haram suka sace, shekara ɗaya da ta wuce a jihar Kaduna.

Ɗaya daga cikin fasinjojin 64, Mukhtar Bala Mohammed ya ce bai taɓa zaton zai kuɓuta ya koma cikin iyalinsa da rayuwa ba.

“Har yanzu idan na ji ƙarar jirgi, sai na firgita, na ruga da gudu,” in ji shi.

Mummunan hari ne da ya yi matuƙar tada hankalin Najeriya da dugunzuma ‘yan ƙasar tun bayan sace ‘yan matan Chibok a 2014 da jerin satar gomman ɗalibai ‘yan makarantun sakandire a jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna.

Da maryacen ranar Litinin ne 28 ga watan Maris ɗin 2022, gungun ‘yan bindiga suka kai wa jirgin ƙasan da su Mukhtar ke ciki, yana tsakiyar tafiya a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja hari.

Wani babban al’amari ne da ya canza rayuwar ɗan kasuwar mai harkar dillancin man fetur gaba ɗaya.

Hukumomi tun a wancan lokaci sun tabbatar da cewa ‘yan Boko Haram ne suka kai harin tare da sace gomman fasinjojin jirgin ƙasan. A cewar Mukhtar Bala sai da ya shafe tsawon kwana 197 cikin dokar daji a hannun masu garkuwar.

Wani babban abu da ya fi bijiro masa a rai yanzu lokacin azumin Ramadan, shi ne yadda suka riƙa shan ruwa bara, idan sun kai azumi da talgen tuwo.

“Talgen tuwo ne za a zuba mana a cikin ɗan ƙaramin kofi. Sai ɗan ƙosai haka tsalli” in ji Mukhtari. “Ka gan ni nan, wallahi ko azumi ɗaya ban sha ba. Duk da yake a cikinmu akwai waɗanda suka sha azumi kamar biyu zuwa uku saboda wahala”.

Ya ce yana farin ciki da ya kuɓutarsa, inda a yanzu yake iya shan ruwa bayan ya kai azumi da nau’in abincin da yake so a cikin iyali.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce “‘yan ta’addan da suka kai harin sun karkatar da jirgin ƙasan daga kan hanyarsa da ƙarfe 7 na maryace bayan sun ɗana abin fashewar da ya tarwatsa wani ɓangare na kwangirin. Daga nan kuma suka buɗe wa taragon jirgin wuta, kafin sace fasinjojin da ke ciki”.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar don cika shekara ɗaya da kai mummunan harin ta ce daga bisani an tabbatar da kashe fasinja tara a harin, sai waɗanda aka sace fiye da sittin, baya ga mutum 20 da suka ji raunuka.

Mukhtar Bala Mohammed, magidanci ɗan shekara 43, ya ce maharan sun kwashe su zuwa ɗan wani tudu inda suka yi jiran fiye da tsawon sa’a ɗaya, kafin su ɗauke zuwa cikin daji kuma suka shafe kimanin sa’a biyar suna tafiya.

Ya ce sun yi rayuwa cikin tsoro da barazana, kuma sun ga rashin ƙauna a tsawon kusan wata bakwai da suka yi a cikin daji.

Read Also:

  • Najeriya ce kan gaba a yawan fitar da man fetur a Afirka cikin watan Mayu – OPEC
  • Tinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi kan ranar dimokuraɗiyya
  • A aƙalla mutum 20 sun rasa rayukansu a saboda hare-hare a Mangu

“Don gaskiya akwai alamun duk a gun za mu halaka…. Ga wasu abubuwa da ke zuwa daga cikin gari, na nuna mana rashin ƙauna. Ko shi ma ya sa duk mun sadaƙar a hannunsu za mu mutu. Ga yawan barazanar cewa za a yanka mu. Suna cewa mu mushirikai ne da sauransu,” a cewar Mukhtar.

Wani lokaci in ji shi, sukan zo, su yi ta yi mana shaguɓe, suna cewa idan mallam ya ce a fara yanka ku, ta kan wane da wane, za a fara.

Harkokinmu duk sun durƙushe
Mukhtar Bala ya ce ya yi imani waɗanda suka sace su ‘yan Boko Haram kamar yadda gwamnati ta shaida tun ana tsare da su a cikin daji. A cewarsa: “Yan Boko Haram ne suka haɗu da wani ɓangare na ‘yan ta’addan daji kuma suka musuluntar da su”.

Ya ce yana cikin sahun ƙarshe na fasinjojin da suka kuɓuta daga hannun maharan ta hanyar wani kwamitin shiga tsakani da hukumomin Najeriya suka kafa don ganin an kuɓutar da dukkaninsu lafiya.

A cewarsa, bayan ya dawo gida ne ya taras duk an sayar da kadarorin da ya mallaka a ƙoƙarin iyali da dangi na ganin an haɗa kuɗaɗen da za a karɓo shi.

“Rayuwa a yanzu ta yi min wahala saboda kusan duk harkokina sun tsaya. Jarina ya karye. Ga shi kuma duk an damfari iyalinmu,” in ji Mukhtar.

Ya ce akwai gida da ya mallaka bayan tsawon lokaci yana tanadi don ya tare da iyalinsa gaba ɗaya, amma bayan ya kuɓuta sai ya taras an sayar da gidan don a kuɓutar da shi.

Haka zalika, harkarsa ta dillancin man fetur ma a yanzu ta durƙushe saboda jarinsa ya karye.

“Ina zuwa asibiti don kula da lafiyata amma saboda yawan shan magani da ƙarancin kuɗi, sun sa na daina zuwa. Matata har yanzu ta kasa sabawa da halin da nake ciki na firgici da tashin hankali.

Kullum yana zuwa asibiti kuma yana shan in ji Mukhar Bala, amma ba ya ganin sauƙi. Wasu ƙuraje masu kama da ƙyazbi duk sun fito masa a kai, ga tsananin ciwon kai da yakan yi fama da shi.

Kuma “Ga mantuwa, sannan abu kaɗan ne zai ruɗa ni, abu kaɗan zan ji ya fusata ni”.

Ya ce rayuwa a yanzu ta kasance mai matuƙar wahala a gare su. Duk da yake, ya ce yana samun tallafi daga abokan arziƙi.

Gwamnatin jihar Kaduna dai ta ce shekara ɗaya bayan aukuwar hari a yankin Kasarami-Audu Jangom cikin ƙaramar hukumar Chikun, har yanzu akwai fasinjojin jirgin ƙasa da ba su je sun karɓi jakunkunansu ba.

Da take sake miƙa saƙon jajentawa ga iyalan fasinjojin jirgin, gwamnatin Kaduna ta ce bayan bincike da aikin ceto, dakarun tsaro a bara, sun gano jakunkunan fasinjoji da dama kuma sun damƙa su hannunta.

Daga bisani dangi ko iyalan fasinjojin jirgi 62 sun je sun karɓi jaka 94 waɗanda suka ƙunshi muhimman takardu da fasfuna da mukullan mota da na gida da kudi da katun cirar kuɗi da wayoyin salula da kwamfyutocin tafi-da-gidanka da litattafai da turarurruka da tufafi da kuma sarƙoƙi da ‘yan kunnaye.

Sai dai har yanzu akwai sauran jakunkuna guda 16 da ba a je an karɓa ba ƙunshe da kayayyaki kamar darduma da litattafai da kuma tufafi.

Ga fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna da aka sace kamar Mukhtar Bala, babban abin da suka ce sun fi so a yanzu, ba tsofaffin kayansu ba ne da akasari ba sa buƙatar su, sai dai ƙwaƙƙwaran tallafi ga lafiya da kuma sake gina rayuwarsu da ta durƙushe.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 3 hours 34 minutes 40 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1444 days 5 hours 16 minutes 5 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
  • TAGS
  • 'Yan Boko Haram
  • Jirgin Kasan Abuja-Kaduna
Previous articleGawuna ya yi wa Abba Gida-Gida fatan alheri a mulkin Kano
Next articleAPC, PDP sun kalubalanci DSS ta kama masu neman dakile rantsar da Asiwaju
Prnigeria

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Zambar N2.2bn: EFCC ta Sake Gurfanar da ɗan Tsohon Shugaban PDP

Magance Karancin Naira: CBN ya Umarci Bankuna da su yi Aiki a Ranakun Asabar da Lahadi

Hatsarin Mota ya yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 25 a Bauchi

Hukumar NITDA ta Gabatar da Satifiket ga Matan da Suka Samu Horo Kan Fasahar Zamani

Ambaliyar Ruwa a Jigawa: Gidauniyar Ƙasar Qatar da ta Malam Inuwa Sun Raba Tallafin Abinci ga Mutane 1,000

An Gudanar Da Bikin Arewa Stars 30 Under 30 2022, Cikin Nasara

Manomi Yayiwa Wata Mata Yankan Rago

‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi da Kashe ‘Yan Sanda Biyu a Anambra

Gidauniyar Malam Inuwa Da Kokarinta Na Ilmantar Da Mutanen Karkara Da Rugage

Gidauniyar Malam Inuwa ta Ɗauki Nauyin Koyar da Ƴa’yan Fulani Al-ƙur’ani

Bincike: Shin Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta ƙirƙiro da Tambayoyi Domin Tantance kungiyoyin Musulmi da Kirista a kidayar 2023? 

An Cire Mukaddashin Babban Akantan Najeriya, Mr Chukwuyere Anamekwe

Recent Posts

  • Najeriya ce kan gaba a yawan fitar da man fetur a Afirka cikin watan Mayu – OPEC
  • Tinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi kan ranar dimokuraɗiyya
  • A aƙalla mutum 20 sun rasa rayukansu a saboda hare-hare a Mangu
  • Najeriya na fuskantar tsaiko kan shirinta na karɓar Dala biliyan 5 daga Saudiya
  • Bom ya kashe masu yawon murnar sallah a Sakkwato

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 3 hours 34 minutes 40 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1444 days 5 hours 16 minutes 5 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Najeriya ce kan gaba a yawan fitar da man fetur a Afirka cikin watan Mayu - OPECTinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi kan ranar dimokuraɗiyyaA aƙalla mutum 20 sun rasa rayukansu a saboda hare-hare a ManguNajeriya na fuskantar tsaiko kan shirinta na karɓar Dala biliyan 5 daga SaudiyaBom ya kashe masu yawon murnar sallah a SakkwatoNan bada jimawa ba za a samu sauyi a ɓangaren man fetur na Najeriya - DangoteSojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda 10 a ZamfaraAn samu tashin gobara a masaukin alhazan Najeriya a Shari MansurGwamnatin Neja na yunƙurin haɗa kai da matatar Ɗangote wajen haƙo ɗanyen man feturJirgin sojoji ya kashe ƴan sa-kai a ƙoƙarin fatattakar ƴanbindiga'Hadarin mota ya yi sanadiyyar matasa 22 'yan asalin KanoGwamnatin Tinubu ta jefa ƴan Najeriya fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci - NLCSojoji sun ce sun hallaka ƴan ta'adda 60 a jihar BornoAn kama mutane 41 kan zargin kashe DPO a KanoRayuwar ƴan Najeriya na ƙara inganta - Tinubu
X whatsapp