Gwamnatin jihar Gombe ta ce ta inganta asibitocin kiwon lafiya daga matakin farko na (PHCs) a wani yunkuri na inganta harkokin lafiya a jihar da kuma inganta manyan asibitoci domin inganta bangaren lafiya.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Habu Dahiru, ne ya bayyana hakan yayi da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya wato NAN a wata ziyarar gani da ido da kamfanin ya kai ranar alhamis.
Read Also:
Haka kuma kwamishinan ya kara da cewa a wani shirin hadin gwiwa da gwamnatin jihar tayi da Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya, (UNICEF) wanda aka gyara asibitocin kiwon lafiya daga matakin farko (PHC) guda 114 domin kara karfafawa gami da inganta matakin lafiyar.
A cewar Mr. Dahiru, gwamnatin jihar na gudanar da aikin jinya don gano tare da tura ta tura yara masu fama da lalurar tamowa da mata masu juna biyu da ba basa samun damar zuwa asibiti domin haihuwa ta hanyar daukar matakai da dama.
Yace sama da ma’aikatan lafiya 600 da suka hadar da Ungozoma, ma’aikatan lafiyar al’umma, CHEW, aka tura zuwa asibitocin na matakin farko PHC a fadin kananan hukumomin jihar 11.
Daga bisani ya tabbatar da cewa daukar wannan mataki ya taimaka wajen rage yawan mutuwar nata masu juna biyu a fadin jihar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 39 minutes 48 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 21 minutes 13 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com