BINCIKE: Me ne gaskiya wani Bidiyo na wani yaro ‘Dan Fulani’ da ke cin Naman Mutane’?

Iƙirari: Wani faifen bidiyo da aka yaɗa, wanda ke nuna wani yaro sanye da rigar ƙungiyar ƙwallon kafa ta Manchester United mai dau]a, yana kuma riƙe da nama a hannunsa da ya yi kama da kafadar ]an Adam. An yaɗa bidiyon ne da ake cewa yaron bafullatani ne.

Bidiyon dake da tsahon minti 1 da daƙiƙa 10 na dauke da hoton wata mata da sautin murya a kasan bidiyon dake ƙarin haske da bayani, in da ta bayyana cewa yaron bafullatani makiyayi ne dake rayuwa a cikin daji.

Ta gargadi masu bibiyarta da su kaucewa irin waɗannan mutane ta hanyar daukar matakan da suka da ce, ta bayyana yadda ya ke cin Naman a yunwace kamar wani mai cin karas. Ta kara da cewa yadda yake cin naman mutane hankali kwance zai iya cutar da kowa. Ta kuma bukaci masu bibiyarta da su yaɗa bidiyon domin ya kai ga wasu.

An hada Bidiyon da wani rubutu mai daukar hankali:

“Dan Fulani na cin naman Mutane; Mun Gama yawo.

Ba iya kasar mu suke buƙata ba- za su cinye mu kamar wasu namon daji.

Waɗanan fulanin sun hada da cin mutane a kan ta’addanci. Ya kamata su fice daga cikin dazukanmu da wuri, ko kuma mun gama yawo. Ya kamata kudanci ya kasance ba wurin zaman mutanen nan ba ne kafin duka su karar da mu.”

TASIRIN KAFAFEN SADA ZUMUNTA

Jaridar PRNigeria ta sake gano wani bidiyon da aka wallafa a shafin facebook, in da aka yi irin wancan iƙirarin amma cikin harshen Yarbanci. Wanda ke cewa Fulani makiyaya na cin naman wanda suka yi garkuwa da shi bayan ‘yan uwansa sun gaza biyan kuɗin fansa. Bidiyon da akalla mutane dubu 9.6K suka kalla yayin da 1.5 suka tofa albarkacin bakinsu a kai, sai kuma mutane dubu 7.3k suka sake yadawa. Ko da ya ke kaɗan cikin waɗanda suka magantu kan wallafar ne suka amince da labarin, da dama sun yi Alla-wadai da wallafar wadda suka kira matsayin yada bayannan ƙarya da ba’a tantance sahihancinsa ba.

Tabbatar da Sahihanci: Domin tabbatar da sahihancin bidiyon da aka yada jaridar PRNigeria ta gudanar wani nazari, in da ta gano cewa muryar da ke kan bidiyon an maye gurbinsa da na asali, wanda aka dora muryar mace wanda salo ne da masu amfani da kafafen sada zumunta suke yi domin daukar hankalin masu bibiyarsu don tara mabiya. Muryar da aka dora akai ta hana gano muryar asali ta bidiyon.

Ƙarin bincike, da suka hadar da yin amfani da hanyar tabbatar da ingancin hoto, da bincike irin solon cin kifin karfasa, ya tabbatar da cewa asalin bidiyon ya fito ne daga  Shafin Tiktok  (@Hadzabe_Lifestyle), wanda ke kawo yanayin rayuwar yau da kullum na Al’ummar Hadzabe, waɗanda ke rayuwa a gabashin Nahiyar Afirka. Kamar yadda aka bayyana a shafin naman da aka ga yaron na ci ba na mutane bane, naman Biri ne, sannan kuma yaron ba bafullatani bane dan ƙabilar Hadzabe.

Bidiyon na asali minti daya ne da daƙika  goma sha shida, idan ka kwantanta da wanda ke yaduwa da ke da tsahon minti daya da daƙiƙa goma. wanda ba’a sauya muryar dake ƙasa ba na dauke da harshen Hadzabe, ba kamar wanda aka dora murya a kai ba dake kokarin rikita al’umma.

Su waye Hadzabe?

Hadzabe ko kuma (Hadza) wasu al’umma ne mafarauta dake zaune a ƙasar Tanzaniya, suna rayuwa ne a yankin Baray a gundumar Karatu da ke yankin Arusha a kasar. Suna rayuwa ne a kusa da tafkin Eyasi daura da tsaunin Serengeti. Sun fito ne daga zuri’ar Bantu, Hadzabe dai mutane ne dake kula da al’ada tsahon dubunnan shekaru.

Al’ummar Hadzabe mutane da suka kware a fannin farauta, wanda suke amfani da makaman da suka hada da hannayensu da suka hadar da kwari da baka matansu da kananan yara kuma sun dogarane wajen cin namun daji matsayin abinci.  Suka ci Nama, Zuma, kayan marmari, da kuma abinci jinsin doya da rogo, ya danganta ta lokaci ko yanayin da ake ciki.

Duk da takurar gwamnati da kuma masu kira zuwa ga addinai na su zauna waje guda sun fara yin noma da kuma addinin kirista, amma da dama cikin al’ummar Hadzabe na gudanar da rayuwa irin ta magabantansu.

Banbancin hannun Mutum da na Biri – Muhimmai

Duk da cewa hannun mutum na kamanceceniya da na biri, amma akwai banbanci na kira:

Babban Ɗan yatsa: babban ɗan yatsan mutum yana da girma, da yake ba shi damar danna wani abu, amma babban ɗanyatsan biri ƙarami ne bai kai na mutum ba.

Ƴan yatsu: ‘yan yatsun mutum basu da tsayi sannan a miƙe suke, ya yin da ‘yan yatsun biri ke da tsayi kuma sun tankwara wanda suke bashi damar hawa tsauni.

Kwarin ƴan yatsu: Hannun mutum na da kwari saboda yanayin tsarin su, amma hannun biri bashi da kwari, da su yake amfani wajen tsalle-tsalle akan bishiya.

A bidiyon dake yawo ya nuna, hannun yana da tsayi, wanda hakan ya nuna cewa kafadar biri ce, ba ta mutum ba.

Kammalawa: jaridar PRNigeria ta tabbatar da cewa yaron da ke jikin wannan bidiyon ba bafullatani ba ne, sannan kuma ba naman mutum yake ci ba. Kuma dan kabilar Hadzabe ne dake kasar Tanzaniya a gabashin Afrika, sannan naman da ake Magana a kai naman biri ne, ba na mutum ba. Sannan muryar da ke kan bidiyon an saka ta ne domin yada labaran ƙarya domin hasala wata kabila da kuma kawo rabuwar kawuna.

Hukunci:  PRNigeria ta yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa “Ɗan Fulani” na cin naman mutum a wancan bidiyon Ƙayar ne da raba kan Al’umma.

PRNigeria

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 9 hours 21 minutes 41 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1444 days 11 hours 3 minutes 6 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com