Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) bangaren da ke kula da dokar kare maradu da ci gaban al’umma, NBA Spidell na neman babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori ministar Al’adu, Hannatu Musawa daga mukaminta bisa zargin karya dokar bautar kasa ta NYSC.
Read Also:
Kungiyar ta kuma bukaci kotun da ta tilasta wa hukumar NYSC ta soke takardar shaidar da aka bai wa ministar bisa zargin bayar da takardar shaidar da ta saɓawa tanadin dokar NYSC.
Wadanda suka shigar da karar sun hada da Shugaban NBA-SPIDEL, John Aikpokpo-Martins, da Sakatariyar NBA-SPIDEL, Funmi Adeogun.
Masu shigar da karar sun yi zargin cewa Musawa ta yi bautar ƙasa na shekara ɗaya bayan ta haura shekaru 30 wanda hakan ya saba ka’idar dokar yi wa kasa hidima.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 7 minutes 56 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 49 minutes 21 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com