Home General Rundunar ‘Yansanda Jihar Kano ta Magantu kan janye Jami’anta a Hukumar karbar...

Rundunar ‘Yansanda Jihar Kano ta Magantu kan janye Jami’anta a Hukumar karbar korafe-korafen ta jihar

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi Karin haske game da janye jami’an ƴan sandan da ke samarwa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tsaro inda ta ce an ɗauki matakin ne saboda za a yi aikin tantance yawan ƴan sandan da ke ƙarƙashin hukumar da kuma fahimtar yanayin ayyukansu tun 2015 da aka tura su yin aiki a hukumar.

Bayanin na ƙunshe cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar inda ta ce za a tantance su ne bayan rahotannin da aka samu ta hannun sashen karɓar ƙorafe-ƙorafe na rundunar da ke nuna cewa ana amfani da ƴan sandan da ke aikin samar da tsaro a hukumar wajen cimma wasu ƙudurori da ba aikinsu ba.

Sanarwar ta ce akwai buƙatar mutane su fahimci cewa ana tantance ma’aikatan domin martani ga rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke watsawa.

Matakin, a cewar sanarwar, ya zama wajibi domin gyara matsalolin da aka gano game da yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta ganin cewa ana amfani da ƴan sandan da aka tura su samar da tsaro wajen yin kame da gudanar da bincike kan ƙararraki, wanda ƙarara ya nuna cewa sun sauka daga tsarin gudanar da aikin da ya rataya a wuyansu – wani abu da ya zama dole a yi gyara a kai.

Rundunar ta ce a baya ma an gudanar da irin wannan aikin tantance ƴan sandan daga lokacin da aka kafa hukumar a 2015 kuma ƴan sandan suka koma bakin aiki bayan kammala aikin.

Sanarwar ta ce babban sufeton ƴan sanda ya umarci ƴan sandan da aka gama tantancewa su gagauta komawa bakin aiki.

Kazalika rundunar ta ce idan har hukumar na son ƙarin jami’an ƴan sanda da za su yi mata wasu ayyukan da ba sa cikin waɗanda babban sufeton ya amince, hukumar na iya neman izini daga shugaban ƴan sandan.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp