Home General Rundunar “yan Sanda sun haramta hawan Sallah a Jihar Kano

Rundunar “yan Sanda sun haramta hawan Sallah a Jihar Kano

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar kano ta ce ta haramta hawan salla yayin bukukuwan Babbar Sallah a jihar Kano.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanyawa hannu kuma aka raba ga manema labarai a jihar.

Sanarwar ta ce rundunar ta dauki wannan matakin ne sakamakon barazanar tsaro da za a iya samu idan an gudanar da hawan sallar.

”Bayan ganawa da duk masu ruwa da tsaki a jihar kano, Rundunar yan sandan jihar kano ta hana yin duk wani hawa a yayin bikin sallah babbar dake tafe” a cewar Sanarwar.

Rundunar ta ce ta haramta hawan a dukkanin fadin jihar kano baki daya.

Rundunar ta bukaci al’ummar jihar da su gudanar da sallar idin su cikin kwanciyar hankali da lumana a inda suke, su kuma cigaba da baiwa rundunar hadin kai don cigaba da inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp