Bincike: Shin da gaske ne masu zanga-zangar #EndBadGovernance sun kwashe kayan abinci da mahaifiyar Dangote ta ajje a store?

Wani bidiyo da aka yada a kafar sada zumunta ta facebook, ya yi ikirarin cewa mahaifiyar attajirin nahiyar Afirka, guda cikin manyan ‘yan kasuwa, Aliko Dangote, Hajiya Mariya Sanusi Dantata, ta yafewa fisatattun matasan da suka balle mata wurin ajiyar kayan abinci, a yayin da ake gudanar da zanga-zangar  #Endbadgovernance a jihar Kano.

Masu amfani da kafar da dama sun yada wallafar a shafin na facebook.

PRNigeria ta gudnar da bincike da wa su alamomi da sunan Nura Ado Faruwa, sakamakon ya nuna babu wata wallafa irin wannan.

Haka kuma, PRNigeria ta fahimci cewa an yi wallafar ne ta asali da wannan suna matsayin wanda ya fara wallafawa, daga bisani ya goge.

PRNigeria ta bincike kafar internet domin gano ko akwai sanarwa ta musamman da aka fitar domin bayyana yafiyar da aka yiwa matasan.

A wata ganawa da PRNigeria ta yi da guda cikin ma’aikatan hajiya Mariya Sanusi ya tabbatar da cewa da gaske ne masu zanga-zanga sun kwashi kaya a wurin ajiyar kayan nata.

“An kwashi kayan abinci da suka hadar da shinkafa, siga, fulawa a wurin ajiyar dake unguwar koki a jihar Kano a ranar farko ta gudanar da zanga-zangar ta ‘EndBadGovernance’ gudana cikin masu taimaka mata da ya bukaci a sakaye sunansa a lokacin da yake ganawa da PRNigeria.

Ya kara da cewa mahaifiyar ta Dangote yanzu haka tana Makka tana gudanar da ibadar Umra, amma bata san da aukuwar lamarin ba.

“Bata ma san an balle mata wurin ajiyar kaya an kwashe kayan ba. Don haka batun cewa ta yafewa wadanda suka dauki kayan ma bata taso ba karya ce kawai.

Kammalawa: saboda wannan bayanin, PRNigeria ta yanke hukuncin cewa da gaske ne an balle wurin ajiyar kayan abinci na Mahaifiyar Dangote a yayin gudanar da zanga-zangar #EndBadGovernance da aka gudanar a fadin kasa, a yayin da ita kuma tana kasar Saudi Arabia tana gudanar da ibadar Umra. Amma labarin da ake yadawa cewa ta yafewa wadanda suka balle wurin ajiyar karya ce kawai daga yau 4 ga watana Agustan 2024

 

PRNigeria

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 14 hours 38 minutes 9 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1444 days 16 hours 19 minutes 34 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com