Hadarin Jirgi ya hallaka mutane 62 a Brazil

Wani haɗarin ƙaramin jirgin sama a Brazil, yayi sanadin mutuwar mutane 62 da ke cikin jirgin.

Jami’ai a ƙasar sun ce babu ko da mutum guda da ya rayu a haɗarin da ya afku a birnin Sao Paulo.

Kamfanin jirgin saman da ya faɗi wato Voepass ya tabbatar da faruwar lamarin cikin daren jiya.

Mahukuntan a ƙauyen Valinhos da jirgin ya faɗi, sun ce iya mutanen da ke cikin jirgin haɗarin ya shafa, amma kuma ya lalata gidaje da sauran gine-ginen da ya faɗa kansu.

A nasa ɓangaren shugaban ƙasar ta Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya jajantawa al’ummar ƙasar kan faruwar lamarin, yana mai cewa sam bai ji dadin yadda zai sanar da faruwar baƙin labarin ba amma ya zama dole ƴan ƙasar su san cewa ƴan uwan su fasinjojin jirgin 58 da kuma ma’aikata biyu sun mutu.

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan dalilin faɗuwar jirgin daga hukumar kula da sufurin jiragen sama ta ƙasar, sai dai kuma faya-fayan bidiyo sun nuna yadda wasu sassan jirgin suka kama da wuta tun yana sama kafin daga bisani ya rikito.

Bayanai sun ce jirgin ƙirar Flightradar 24 wanda aka samar a shekaar 2010 na da matuƙar ƙarfi da kuma juriya wajen aiki, kuma an samar da shi ne a jihar Parana ta ƙasar.

sao dao Gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki kasar, inda shugaban kasar lula De silva ya bukaci yin shiru na wani lokaci.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 8 hours 19 minutes 24 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 10 hours 49 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com