Wani bidiyo da aka yaɗa a manhajar WhatsApp, ya yi ikirarin cewa wasu limamai da malaman majami’u a jihar Filato sun ja ragamar gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.
Mafi akasarin mutanen na tafiya ne sanye da baƙaƙen kaya, dauke da alamun addinin kirista da alamar gicciye (cross) a wuyan su, a gefe kuma ga wani mutum sanye da kayan hausawa. Sun riƙe hannu yayin da suke gudanar da zanga-zangar.
PRNigeria ta raba bidiyon gida-gida inda ta gudanar da binciken sahihancin hoto ta hanyar yin amfani da salon (reverse image search).
Sakamakon ya nuna cewa bidiyon ya fito ne daga jihar ta Filato a lokacin da ake gudanar da tattakin zaman lafiya, bisa jagorancin shugaban ƙungiyar CAN Rev. Polycarp Lubo, sai kuma shugaban majami’ar ECWA Rev. Dr. Stephen Panya, ya shiga ciki da sauran shuwagabannin kungiyoyin kirista a watan Janairun 2024. Wanda tattakin na su na nuna rashin gamsuwa da kisan mutane sama da 200 da aka yi a ranar bikin kirsimeti a kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi dake jihar.
Read Also:
Tattakin da ya sami halartar mabiya addinin kirista da dama da hadin gwiwar mazauna yanki, wanda suka taro a gidan Gwamnatin jihar da ke garin Jos, ya yin da gwamnan jihar Caleb Mutfwang ya tarbe su.
Shuwagabannin kiristocin sun buƙaci gwamnatin jihar ta dauki matakin da ya dace na kare rayuka da dukiyoyin al’umma ga wadanda ke hallakasu ba ji ba gani.
Wani bincike ya nuna cewa mutane da dama sun wallafa bidiyon a shafukan su na X wanda aka fi sani da twitter, tare da laƙabin “tattakin zaman lafiya daga shuwagabannin kirista” #StopTheKillings.
PRNigeria ta jiyo wakokin ibada na addinin kirista cikin harshen hausa, suna kuma kaɗa korayen ganye da ke hannayen su.
KAMMALAWA: bisa ga hujjojin da PRNigeria ta tattara sun tabbatar da cewa Limamai da Malaman Majami’u basu jagoranci wani gangami ko tattaki na ‘EndBadGovernance’ a garin Jos da ke jihar Filato ba.
Amma, abin da ma su iƙirarin suka gani matsayin zanga-zanga, to tattaki ne na zaman lafiya na daruruwan al’umma mabiya addinin kirista a kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi suka gudanar.
Don haka, PRNigeria ta tabbatar da ikirarin da aka yi na cewa malaman Addini sun haɗa gwiwa don kalubalantar yadda Tinubu ke gudanar da Gwamnatinsa Karya ce a bayyana ne.
By PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1462 days 14 hours 41 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1444 days 16 hours 23 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com