Home General Kotu ta tura jagororin Zanga-Zanga gidan gyaran hali a jihar Katsina

Kotu ta tura jagororin Zanga-Zanga gidan gyaran hali a jihar Katsina

Wata kotu a jihar Katsina ta tura 7 daga cikin jagororin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a ƙasar, gidan yari tsawon wata ɗaya.

Wani makusancin biyu daga cikin jagororin ya shaodawa kafar BBC cewa, a ranar Juma’a 9 ga watan Agusta 2024, rundunar ‘yansanda ta jihar ta gurfanar da Kwamared Habibu Ruma da Kwamared Kabir Shehu ‘Yanɗaki da kuma wasu mutum biyar a gaban kotun majistare a birnin Katsina, inda ta tuhume su da laifukan da suka haɗa da tarzoma da sata da kuma ɓarnata kayan gwamnati.

Bayan an karanta musu laifukan da ake tuhumarsu da su, ”sai kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar 11 ga wata mai zuwa, Satumba, 2024 tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare mutanen bakwai a gidan kaso, zaman waƙafi.

A Najeriya an gudanar da zanga-zanga ta gama-gari daga ranar 1 ga watan Agusta, 2024 zuwa 10 ga watan na Agusta 2024, saboda matsaloli da suke addabar ƙasar, waɗanda suka haɗa da tsadar rayuwa da rashin tsaro musammana a arewacin da neman shugabanci na gari.

Sai dai yayin da zanga-zangar ta kasance cikin lumana a wasu jihohin, a wasu kuwa ta rikiɗe ta zama tarzoma inda aka riƙa sace-sace da ɓarnata kayan gwamnati da na ‘yan kasuwa da ɗaiɗaikum mutane.

Tarzomar ta kuma yi sanadin kashe mutane da jikkata wasu da dama.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp