Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ziyarci Dam din Kafinchiri a karamar hukumar Garko, domin ganin yadda aiki ke gudana, wanda aka bayar da shi a yunkurin kawo sauyi a fannin noma a jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Lahadi.
Sanarwar tace aikin, wanda darajarsa ta kai Naira biliyan 2.5, an yi shi ne da nufin bunkasa noman rani da damina, da inganta samar da abinci, da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada muhimmancin aikin noman na Kafinchiri, inda ya bayyana hakan a matsayin wani muhimmin bangare na kokarin gwamnatinsa na bunkasa noma a jihar Kano.
Read Also:
Ya bukaci mazauna garin Garko da kewaye da su yi amfani da damar da aikin zai bayar domin inganta tattalin arzikin su da jihar baki daya.
A wani labarin kuma, Gwamnan ya sanar da kwace kwangilar aikin hanyar karamar hukumar Garko mai tsawon kilomita biyar saboda gazawar dan kwangilar na dawowa bakin aiki.
Ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a baiwa wani mai kwazo kwangilar aikin don tabbatar da kammala aikin a kan kari.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma kuduri aniyar samar da cibiyar lafiya ta zamani a garin Garko, da nufin kusantar da harkokin kiwon lafiya ga jama’a.
Ya nuna jin dadinsa bisa goyon bayan da al’ummar yankin suke ba shi tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba gudanar da aiyukan cigaba a jihar .
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 10 hours 16 minutes 5 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 57 minutes 30 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com