Tawagar Kano Pillars FC, wacce ta lashe gasar Nigeria Premier Football League, NPFL, sau hudu, ta sanar da sababbin ‘yan wasan da ta dauka a hukumance gabanin kakar wasanni ta 2024/25.
An gudanar da taron bikin gabatar da sabbin ‘yan wasan a filin wasa na Sani Abacha a ranar Laraba, 4 ga Satumba, 2024, tare da halartar Shugaban tawagar, Alhaji Ali Muhammad Na Yara Mai Samba, gami da wasu daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa.
A shirye-shiryen da take yi don sabuwar kakar wasannin, tawagar ta dauki sabbin ‘yan wasa guda goma sha biyu, tare da mai da hankali kan wasu muhimman wurare don kara karfin tawagar.
Read Also:
Wannan shiri ya nuna kudirin Kano Pillars FC na dawo da matsayinta na babbar tawagar ƙwallon kafar Nijeriya.
Sabbin ‘yan wasan sun hada da masu tsaron gida guda uku, wasu masu tsaron baya, ‘yan wasan tsakiya, da ‘yan wasan gaba, wadanda suka hada da ‘yan wasan cikin gida da kuma na kasashen waje.
Bugu da kari baya da sababbin ‘yan wasan da aka dauka, tawagar ta ci gaba da rike ‘yan wasa ashirin daga kakar wasannin da ta gabata, wanda hakan zai haifar da taka leda mai kyau ga tawagar.
Kano Pillars FC za ta fara buga gasar NPFL ta 2024/25 a ranar 8 ga Satumba, 2024, inda za ta rika buga wasanninta na gida a filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina a matsayin wucin gadi, saboda gyare-gyaren da ake yi a filin wasa na Sani Abacha.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 2 hours 32 minutes 18 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 4 hours 13 minutes 43 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com