Home General Majalisar Dattawan Najeriya za ta binciki zarge-zargen Tchiani kan Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya za ta binciki zarge-zargen Tchiani kan Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya ta ba da umurnin binciken zarge zargen da shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya yi na cewa gwamnatin Najeriya na haɗa kai da Faransa wajen kawo cikas ga tsaron ƙasarsa.

Umarnin na zuwa ne bayan wani ƙuduri da shugaban kwamitin tsaro na majaliar, Sanata Shehu Buba ya gabatar, inda ya jaddada cewa babban abin damuwa shi ne yadda Tchiani ya zargi mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasa, Ahmed Rufai, da hannu dumu-dumu wajen yi wa ƙasarsa bita-da-ƙulli.

Cikin zarge-zagen nasa, Tchiani ya ce gwamnatin Najeriya na taimaka wa ƙungiyar ƴan ta’adda ta Lakurawa da ke arewa maso yammacin ƙasar, wajen kafa sansanoni a Sokoto da Zamfara da kuma Kebbi, sannan suna amfani da wasu sansanonin sojoji a Najeriya domin kai hari kan bututun man Nijar da kuma kawo barazanar tsaro a ƙasarsa.

A martaninsa a zaman majalisar, mataimakin shugaban majalisar, sanata Barau Jibrin wanda ya jagoranci zaman ya amince da matsayar da ta buƙaci kwamiti kan tsaron ƙasar da kwaminitin harkokin ƙasashen waje su gudanar da bincike su kuma gabatar da rahoton nan da makonni huɗu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp