Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa za ta samar da cibiyoyi na musamman ga almajirai da masu buƙata ta musamman domin yin buɗe baki a lokacin azumin Ramadan.
Gwamnan ya bayyana haka ne a sa’ilin da ya ƙaddamar da wani sabon masallacin juma’a.
Ya ce “mun ci alwashin faɗaɗa cibiyoyin buɗe-baki zuwa wuraren da babu su domin amfanin mabuƙata a cikin al’umma.
Ciyarwa a lokacin azumin Ramadana wani abu ne da yawancin jihohin arewacin Najeriya ke gudanarwa a kowace shekara, sai dai batu ne da ke janyo muhawara sanadiyyar maƙudan kuɗaden da ake kashewa.
Yayin da wasu ke kallon lamarin a matsayin tallafawa wa al’umma, wasu na ganin cewa za a iya amfani da kuɗaɗen wajen aiwatar da ayyukan gwamnati waɗanda za su amfani al’umma.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 16 hours 10 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 17 hours 51 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com